
Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na shan suka kan amfani da karfi a mulkinsa
An kama wani marubuci a kasar Masar bayan ya wallafa wani littafi da ke kalubalantar manufar tattalin arzikin gwamnatin kasar.
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ce a yanzu marubuci Abdel-Khaleq Farouq, da wanda ya buga littafin nasa, Ibrahim el-Khateib, na fuskantar tuhumar yada “labaran karya”.
AP ya ce littafin mai suna “Is Egypt Really a Poor Country?” (Shin da gaske ne Masar matalauciyar kasa ce?), an watsa shi ne a yanar gizo amma ba a kaiga fara sayar da butun hannu ba.
Rahotanni sun ce littafin ya kunshi sukar Shugaban kasar Abdel-Fattah el-Sissi da manufofin tattalin arzikinsa.
Farouq ya kalubalanci ikirarin cewa Masar matalauciya ce a don haka tana bukatar janye tallafin da gwamnati ke bai wa ‘yan kasar.
An kama Farouq da marubucin littafin nasa ne ranar Lahadi inda aka yi masa tambayoyi na kusan sa’o’i bakwai, kamar yadda lauyansa ya shaida wa AP.
Ko a kwanakin baya ma an tsare wata mata bayan ta bayyana yadda ta ce wani mutum ya ci zarafinta ta hanyar yunkurin yin lalata da ita.
Kasar Masar ta kafa dokar hana yada labaran karya, sai dai wasu na zargin ana amfani da dokar wurin takurawa ‘yan adawa da kuma dakile fadar albarkacin baki.