
Wani shafin intanet ne ya fara yada labarin
A makon da ya gabata ne akai ta yada wani sako a shafin Twitter da ke nuni da cewa Ministan Yada Labaran Najeriya, Lai Mohammed, ya ce kasar za ta kaiwa Isra’ila hari muddin ba ta mika mata jagoran ‘yan aware na yankin Biafra ba, Nnamdi Kanu.
Wannan batu, wanda ya ja hankalin jama’a da dama, ya zo ne bayan rahotanni suka ambato bayyanar Mr Kanu, wan da aka dade ba a ji duriyarsa a birnin Kudus.
Sai dai ministan ya karyata wannan labari inda ya ce babu inda ya ayyana cewa Najeriya za ta kaiwa Isra’ila hari yana mai cewa labarin boge ne.
Alhaji Lai Muhammad ya ce fitowar da Nnamdi Kanu ya yi a Isra’ila ta wanke gwamnatin kasar wadda jama’a da dama ke zarginta da boye shi ko ma kashe Mr Kanu, bayan a kwashe kusan shekara a nemansa.
Kagoran na kungiyar IPOB wacce ke rajin ganin an kafa kasar ta Biafra a yankin Kudu maso Gabashin kasar, ya yi batan-dabo ne a bara bayan wani samame da jami’ar tsaro suka kai kauyensu a jihar Abia.
Mr Kanu ya tsallakewa belin da aka bashi ne a shari’ar da ake yi masa kan zargin amanar kasa, lamarin da ya musanta.
Jami’an gwamnati sun ce a shirye su ke domin komawarsa kasar, kamar yadda ya yi ikirarin yi.