
Razak Atunwa ya ce bai saba wata ka’ida ba
A farkon makon nan ne jaridar Premium Times ta wallafa wani bincike da ya nuna cewa dan takarar gwamna na jam’iyar PDP a zaben 2019 a jihar Kwara ya gabatar da takardar shaidar hidimar kasa ta bogi domin ya cika sharuddan jam’iyyar na tsaya mata takara.
Razak Atunwa, wanda dan majalisar tarayya ne kuma na hannun damar shugaban majalisar dattawan Najeria, Bukola Saraki, ya musanta zargin.
Sai dai binciken da Bindiddigi ya gudanar ya gano cewa jam’iyyar ta PDP ta bai wa Mr Atunwa wani dan lokaci a kan ya kare kansa dangane da wannan rahoto da aka wallafa.
Kuma wasu majiyoyi sun tabbatar mana cewa, jam’iyyar na iya canja shi idan har ya gaza bayyana gamsasshiyar hujjar da za ta nuna cewa rahoton na Premium Times ba gaskiya ba ne.
Kawo yanzu jam’iyyar PDP ba ta bayyana matsayinta a hukumance ba kan wannan batu.
Rahotanni sun bayyana cewa Mr Atunwa ya yi karantun fannin sharia a Jamiar East London kuma ya kammala a shekarar 1992 yana dan shekara 23, amma sai ya ki komawa Najeriya domin yin hidimar kasa abin da ya sabawa sashi na biyu na dokar hukumar NYSC.
Sai a shekarar 2005 ne ya koma kasar lokacin da aka bashi mukamin kwamishina a jihar ta Kwara.
Ministan Buhari ya garzaya kotu
Abin da ba a tantance ba shi ne ko Mr Atunwa ya gabatar da wata takarda daga hukumar hidimar kasa ta NYSC kafin a damka masa wadancan mukamai da ya rike.
Abin da ya fito fili dai shi ne yadda ya rubuta wa PDP cewa ya karbi shaidar yafiya ta hidimar kasa a shekarar 1996 kuma aka sami takardar da sanya hannun Birgediya Janar Walta Oki wanda aka hakikance cewa ya zama shugaban hukumar ne a shekarar 2002.
Wannan dambarwa na zuwa ne bayan da aka yi zargin makamanciyarta ga tsohuwar Ministar Kudin kasar Kemi Adeosun, al’amarin da ya sa ta yi murabus ba a san ranta ba, sannan ta fice daga kasar ba tare da an hukunta tata ba.
Hakazalika a halin yanzu akwai irin wannan zargi akan Ministan Sadarwa Adebayo Shitu, wanda ya bayyana cewa bai halarci aikin yi wa kasa hidima ba.
Ministan ya yi jawabi ne bayan da Premium Times ta bankado cewa bai sanya kwafin takardar shaidar yi wa kasa hidima ba a takardunsa da ya aikewa majalisar kasa ya yin da aka tantance shi a mukamin ministan.
Wannan al’amari ya shafi ministan a lokacin da jam’iyarsa ta APC ta ki tantance shi domin tsaya mata takarar gwamna a jihar Oyo matakin da ministan yake kalubalanta a Kotu.
Kodayake ministan bai sauka daga mukaminsa ba, amma fadar shugaban kasa ta fitar da wani jawabi mai kama da gugar-zana ga ministan, inda take cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba ya sha’awar sauke kowane minista daga mukaminsa amma yana burin ganin duk wanda yake da kashi a gindi, ya ajiye mukaminsa bisa radin kansa/kanta.