
Kwanan nan Zainab Ahmed ta karbi ragamar shugabancin ma’aikatar kudin kasar
A farkon makon nan ne takaddama ta barke a Najeriya bayan da wasu kafafen yada labarai suka ambato ministar kudin kasar na cewa “gwamnati na shirin fito da tsarin kayyade iyali a kasar”.
Kafofin sun ruwaito cewa Zainab Ahmed ta furta hakan ne a wani taron farfado da tattalin arzikin kasa, inda ta ce “Ina ganin da hadin kansu, gwamnati tana kokarin bullo da wani shiri wanda zai iya taikata yawan yaran da mace za ta iya haifa”.
Mun bi diddigin wannan batun domin fayyace gaskiyarsa.
Nan take dai wannan lamari ya jawo muhawara a tsakanin ‘yan kasar, wacce ke da masu bin ra’ayin ‘yan mazan-jiya da dama.
Sai dai sa’o’i bayan fitar wannan rahoto, sai ministar, wacce aka ce ta yi jawabin ne a wurin wani taro a Abuja, babban birnin kasar, ta yi watsi da rahotannin, tana mai cewa “sam ba haka tab fada ba”.
Ta wallafa a shafinta na Twitter @ZShamsuna in da ta ce “gwamnatin tarayya tana kokarin neman goyon bayan masu ruwa da tsaki da suka hada da shugabannin gargajiya da na addini wajen ganin ana samun tazarar haihuwa.”
“Babu inda muka ce za mu taikaita haihuwa. Shin mene ne tazarar haihuwa? Tazarar haihuwa ita ce ba da wasu ‘yan shekaru tsakanin bayan an haihu kafin a sake daukar wani cikin”.
Wannan kalamai da ministar ta wallafa ya sa wasu daga cikin kafafen da suka rawaito labarin na farko sake rubuta wani mai kunshe da gaskiya da kuma ainahin abin da ta fada.
Mun fahimci cewa ministar ce ke da gaskiya musamman ganin wadancan kafafen yada labarai ba su ja da musantawar da ta yi ba, sannan suka dauki sabbin kalaman nata.