
Shugaba Buhari da ministocin sufuri lokacin kaddamar da jirgin kasa na Abuja-Kaduna
A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu wani aikin gina kasa da gwamnatocin baya suka aiwatar a kasar daga shekarar 1999 zuwa 2014.
Wadannan kalamai dai sun ja hankali a don haka muka bi diddiginsu domin tantance gaskiyar maganar ko akasin haka.
Abinda Buhari ya ce
Da ya ke magana a lokacin da ya ke bankwana a fadarsa ga jakadan Birtaniya a Najeriya wanda ya kammala aikinsa, Shugaba Buhari ya ce:
“Mun mayar da hankali wajen manyan ayyukan gina kasa; kamar layukan dogo, da hanyoyi, da wutar lantarki da sauransu.
“Ina ma ace duk munyi wadannan ayyukan lokacin da muke samun kudi. Abin da kasar nan ta samu daga shekarun 1999 zuwa 2014 yana nan a rubuce, sai dai babu wani aikin gina kasa da aka yi.
“A yanzu muna yin ayyuka da dama duk da cewa kudaden da muke da su ‘yan kalilan ne, amma za mu ci gaba da yin iya kokarinmu”.
Ina gaskiyar wannan ikirarin nasa?
An yi shugabanni uku a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2014, Olesegun Obasanjo, Umar Musa ‘Yar’adua da Goodluck Jonathan, duka na jam’iyyar PDP.
Shafin Bindiddigi ya gano cewa ikirarin Shugaba Buhari na cewa babu wani babban aikin gina kasa da aka aiwatar a wadancan shekaru ba gaskiya ba ne, domin bincikenmu ya nuna cewa akwai ayyuka da aka yi da dama a fadin kasar:
Shugaba Jonathan ya kaddamar da tashar wutar lantarki da aka gina ta Olounshogo mai samar da megawat 700, wacce a lokacin gwamnati ta ce ita ce ta biyu mafi girma a kasar.
Kafin wannan, gwamnatin ta Jonathan ta kaddamar da wasu kananan tashoshin biyu na Geregu da Omotosho a jihar Kogi a 2013.
Mr Jonathan ya kuma kaddamar da gadar sama a birnin Kano, wacce ake wa lakabi da Gadar Lado a kan titin Zaria Road. Akwai kuma makamanciyarta da gwamnatin tarayya ta yi a shataletalin Na’ibawa.
Haka nan kuma gwamnatin ‘Yar’adua ce ta fara aikin titunan shiga Abuja na Murtala Mohammed da Umaru Musa ‘Yar’adua masu layuka goma-goma, wanda Jonathan ya kammala.
Haka kuma a lokacin ‘Yar’adua ne aka fara aikin jirgin kasa na cikin birnin Abuja wanda Jonathan ya ci gaba har zuwa sama da kashi 60 cikin dari sannan Buhari ya karasa ragowar.

Shugaba Goodluch Jonathan lokacin da ya ke duba aikin jirgin kasan Kaduna-Abuja a 2015
Hakazalika jirgin kasan da ke jigila daga Kaduna zuwa Abuja Obasanjo ne ya fara aikin, sannan ‘Yar’adua da Jonathan suka ci karfinsa yayin da Buhari ya kammala kalilan din da ya rage.
A lokacinsu ne kuma aka farfado da zirga-zirgar jiragen kasa daga Kano zuwa Legas.
Haka kuma gwamnatocin baya ne suka bayar da kwangilar gina sabbin wuraren sauka da da tashi a filayen jiragen sama na Legas, da Fatakwal da kuma Kano. Aikinsu ya yi matukar nisa lokacin da Buhari ya hau mulki, kuma a watan Oktoba ne ya kaddamar da na Fatakwal.
Hanyar Nyanya zuwa Abuja
A shekarar 2007 ne Shugaba Obasanjo ya bayar da kwangilar aikin titin da ya tashi daga Kano zuwa Maiduguri da kuma na Abuja zuwa Lakoja, kuma gwamnatocin da suka biyo bayansa suka ci gaba da su.
A wadannan shekaru ne kuma aka yi hanyar Nyanya zuwa cikin garin Abuja tare da gina manyan gadojin sama domin rage cunkoso.
A shekarar 2003 ne gwamnatin Obasanjo ta kafa Hukumar Kula da Gyaran Manyan Hanyoyi ta Kasa (Ferma), wacce a shafinta na intanet ta ce ta gyara hanyoyi sama da 500 da nisansu ya kai kilomita 13,000 a ‘yan shekarunta na farko kawai.
Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.
Wadannan kadan ne daga cikin ayyukan da muka zakulo domin tantance gaskiyar kalaman na Shugaba Buhari, kuma wannan ya nuna cewa kalaman nasa ba su da hujja, a don haka na rikitar da tunanin mutane ne kawai.
Ku ci gaba da kasancewa da shafin Bindiddigi domin sanin gaskiyar labaran da ake watsawa da kure-karyar da wasu ke yi a shafukan intanet da sauran kafafen yada labarai.