Wani shafin intanet na Nigerian Diary ya bullo da wata gasa wadda za ta bai wa masu zabe a Najeriya damar bin diddigin alkawuran da ‘yan siyasa kan yi wa jama’a yayin neman kuri’arsu a babban zaban kasar da ke tafe a badi a duk fadin kasar.
Shafin, wanda ke yada labarai a yanar gizo, ya wallafa a shafinsa na Twitter @NigerianDiary cewa, gasa ce da aka kirkira tare da hadin gwiwar Gidauniyar MCArthur Foundation ta Amurka domin samar da tattaunawa mai amfani game da aikace-aikacen siyasa a matakin jihohi da na kasa baki daya.
Gasar dai ta rubutu ce wadda ta bukaci masu zabe da su rubuto takaitacciyar makala kan wani daftari ko alkawari na wani dan siyasa da ya yi a matakin kasa ko na jaha, wanda hakan zai ba da damar lashe kyautar tsabar kudi har Naira dubu 10,000 a duk mako ga wadanda suka yi nasara.
Wadanda saka fito da wannan tsari na ganin cewa zai taimaka wurin dakile labaran karya da aka saba yadawa musamman a lokutan zabe da bayansa, ta hanyar karfafa gwiwar wadanda ke da alhakin yada irin wadannan labaran da su yi bincike kan labarai na gaskiya domin samun nasarar lashe kyautar.
Wasu daga cikin dokokin gasar sun hada da; makalar dole ne ta kasance ta kashin kai sannan kuma kar ta wuce kalmomi 800 zuwa 1,000, sannan a aika zuwa adireshinsu nfo@nigeriandiary.com.
Za a sanar da wadanda suka yi nasara a duk sati kuma za a wallafa makalar tasu a shafin intanet na www.nigeriandiary.com.
Masana dai na ganin cewa wannan ka iya yin tasiri kan yadda masu amfani da shafukan zumunta ke tafka muhawara a kullum game da al’amuran siyasa a Najeriya, wanda a mafi yawan lokaci ke karkewa da zage-zage, yada kalaman kanzon-kurege, ko kuma rigima.