Akwai hanyoyi 10 da za a iya bi a matakin farko domin tantance “labaran karya” ko na boge.
Labaran kanzon-kurege na da wahalar sha’ani, hakan ta sanya wata cibiyar bayar da tallafi domin yaki da labarun karya ta Birtaniya tare da hadin gwiwar kamfanin sada zumunta na facebook suka fitar da wasu dabaru 10 da za su taimaka a matakin farko wajen tantance sahihancin bayanai.
1. Yin taka-tsantsan game da kanun labari
A mafi yawancin lokuta, labaran karya su kan dace da “Kanu” mai jan hankali da girgiza zuciya. Idan har zuciyarka ta yi dar akan kunshin bayanan “kanun labari” to akwai alamar tababa akan nagartar labarin.
2. Lura sosai da manhajar labari
Manhaja mai shigar giza-gizai alama ce ta zargi akan sahihancin labari ko bayani. Yawancin dandalin da ke baza labaran karya ya kan kirkiri manhajar da ke kamanceceniya da wata sahihiyar kafar sadarwa. Lallai ne a bi diddigin manhaja domin tabbatar da ingancin tushen labari.
3. Binciki tushen labari
A tabbatar da cewa wata nagartacciyar kafa ce ta buga labarin wadda ba a shakkar ingancinta. Idan aka sami labari daga wata sabuwar kafa to a bincika mamallakanta a shafinta na yanar gizo domin samun karin haske.
4. A lura da tsarin zubin labari
Mafi yawancin shafukan da ke buga ‘labaran karya’ bas u damu da kyautata tsarin zubin labari ba ko lura da kiyaye ka’idojin rubutu. Akan sami kura-kurai da yawa a wannan fannin.
5. A yi la’akari da hotuna
Yawancin labaran karya suna dauke ne da sandararru ko hotuna masu motsi wadanda aka sarrafa. A wasu lokutan kuma sukan saka sahihin hoto amma wanda bas hi da alaka da labarin. Ana iya bin asalin hotunan domin tantance su.
6. Duba kwanan wata
Labaran karya kan kunshi cin karo da al’amuran da aka zayyana cewa sun faru da kuma ranakun da aka gabatar da su. A kan alankanta rana wacce ta sha bambam da aikin da aka jingina mata.
- Hanyoyi hudu da za a yaki labaran boge
- Zaben 2019: An bai wa jama’a damar bindiddigin alkawuran zabe
- Najeriya: Kayyade iyali ko ba da tazara?
7. Kodayaushe a bincika hujjoji
Akwai matukar bukatar bincika tushen labarin da aka gabatar domin gano gaskiyar ikirarin marubuci. Rashin bincike ko dogaro akan wani kwararre da aka jingina labarin gare shi kuma ba a ambaci sunansa karara ba, alamace ta rashin tabbas akan gaskiyar labarin.
8. Lura da wasu kafofin
Rashin samun wata kafa da ta rawaito makamancin labarin, alama ce ta zargi akan sahihancinsa. Amma idan akwai wasu kafafe da aka amince da nagartarsu suka goyawa labarin baya ta hanyar fitar da irinsa to akwai alamun kanshin gaskiya a cikinsa.
9. Ko labarin ya yi kama da wasa?
A mafi yawancin lokuta, labaran karya suna wahalar da mutum wajen tantance wa shin labaran nishadi ne ko na barkwanci. Cikakken bincike akan salo ko zubin labarin zai taimaka wajen gano cewa ba labarin wasa ba ne.
10. Kirkirarrun labarai
Ayi duba na tsanaki akan labaran da ake karantawa, sannan a tabbatar cewa wadanda aka tabbatar da nagartarsu ne kadai ake yadawa.