Wannan hoton na Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yana tattaunawa da wata dattijuwa da kuma wani rubutaccen sako ya yi farin jini sosai a wurin mutane da dama.
An rinka yada shi musamman a dandalin sada zumunta na WhatsApp, inda aka rinka yabawa shugaban saboda fito da wasu “sabbin tsare-tsare na tallafawa tsofaffi”.
Matakan dai an ce sun hada da bayar da muhalli kyauta, da kulawa da lafiyar tsofaffin, da kuma tallafin dala 300 na Amurka a kowanne wata har karshen rayuwarsu.
Hakazalika hoton na dauke da bayanin cewa za a rinka bai wa tsofaffin kujerar Aikin Hajji kyauta sau daya.
Ina gaskiyar batun?
Wannan dai shi ne dalilin da ya sa aka rinka yada hoton da kuma sakon da yake dauke da shi, inda jama’a suka rinka yabawa Mr Erdogan.
Dama dai farin jinin shugaban na karuwa a tsakanin wasu Musulmai saboda rawar da suke ganin yana takawa a fagen sisayar duniya.
Sai dai binciken da Bindiddigi ya yi, ya gano cewa dama Turkiyya na da shirin tallafawa al’ummarta, amma labarin da ake yadawa na baya-bayan nan ba ya cikin tsarin kasar.
A don haka labari ne na kanzon-kurege ne.
Haka kuma an dauki hoton ne a shekarar 2015 lokacin da Shugaba Erdogan ya kai ziyara wata makabarta domin yin addu’a a kabarin iyayensa da ke can.
Jama’a sai a yi hattara wurin yada labarai ba tare da an bincika tushensu ba. Za ku iya tuntubarmu idan kuna so a fayyace muku sahihancin labarin da ya shige muku duhu.
Shin kun ci karo da wani labari, hoto ko bidiyo da ba ku yarda da sahihancinsa ba kuma kuke son a bi muku diddiginsa? Ku turo shi zuwa lambar WhatsApp din shafin http://www.bindiddigi.com +2349027450542 domin a bincika muku sahihancinsa. Sai mun ji daga gare ku. Za kuma ku iya latsa wannan shafin domin shiga dandalin Ma’abota shafin Bindiddigi a WhatsApp: https://chat.whatsapp.com/KFgHYjlqoaUAfjfyxCLDXO