Shafin Facebook ya yi kaurin-suna a matsayin dandalin da ake yada labaran karya da wasu ma’abota shafin kan yi, sai dai dandalin sadarwa na WhatsApp shi ma ba kanwar lasa ba ne idan ana maganar labaran kanzon-kurege.
Tin daga lokacin da masu amfani da shafin sadarwar na sirri suka kai yawan miliyan 1,000 a shekarar da ta wuce, kuma bugu da kari shafin ya sirranta tattaunawar da mutane kan yi tsakaninsu (end-to-end encryption), sannan ya fadada yawan mambobi a kowanne guruf zuwa 256, shafin ya zama wata matattarar jita-jita da tayar da husuma.
Akwai hanyoyi bakwai da ma’abota shafin na WhatsApp za su iya bi wurin rarrabewa tsakanin aya da tsakuwa game da labaran da ake yadawa:
1. Ka zama mai tsantseni yayin tura wani bayani har sai ka tabbatar da gaskiyar abin da ya kunsa. Shafin Décodeurs suna da bayanai kan yadda za ka/ki zama mai tsantseni a shafukan sadarwa.
2. Bincika babban maudu’in da sakon ke dauke da shi a shafukan matambayi ba ya bata na (Google, Bing da sauransu), za ka iya samun wata makala ko labari da aka rubuta kan maudu’in domin tabbatar da gaskiyar abin da sakon ya kunsa.
3. Za ka iya bankado labaran karya da kanka idan ka yi amfani da shafin binciken hoto na Google reverse image search, da Tin Eye, da kuma Fake Image Detector. Idan kuma fefan bidiyo ne sai ka dauki hoto (screenshot) ka dora kan shafin Intanet na daya daga wadancen adireshin. Ga yadda za kai amfani da su.
4. Nemi hanya mafi sauki wadda za ka tuntubi kafofi wadanda aikinsu ne tona asirin labarai marasa tushe ta hanyar kiran waya ko tura sako. Da zarar ka yi hakan za su bincka gaskiyar al’amarin.
5. Ka tura da duk wani sako, ko barkwanci, ko hoto, ko fefen bidiyo da kake tantamar
sahihancinsa zuwa ga masu tantance labaran karya da ka sani a kasarku. Bayan sun gudanar da bincike sai ka yada sakamakon binciken zuwa cikin gurup din da ka fara ganin abin. Kuna iya aikowa Bindiddigi labaran da kuke bukatar a tantance, a adireshin email: bindiddigi@gmail.com ko ta twitter @bindiddgi
6. Yi kokari ka duba shafukan sada zumunta na kamfanoni ko ma’aikatu da aka ambata a cikin labarai marasa tushe domin a wasu lokutan sukan yi watsi da irin wadannan labaran su da kansu.
7. Za ka iya hada gwiwa da masu dakile labaran kanzon-kurege domin kai ma ka taimaka wurin yada labarai na gaskiya.
Shin kana da wata hanyar dakile labaran karya wadda ba mu saka ba a nan? Za ka iya turo mana ta hanyoyin tuntubarmu a wannan shafi. bindiddigi@gmail.com ko @bindiddigi
Shin kun ci karo da wani labari, hoto ko bidiyo da ba ku yarda da sahihancinsa ba kuma kuke son a bi muku diddiginsa? Ku turo shi zuwa lambar WhatsApp din shafin http://www.bindiddigi.com +2349027450542 domin a bincika muku sahihancinsa. Za kuma ku iya latsa wannan shafin domin shiga dandalin Ma’abota shafin Bindiddigi a WhatsApp: https://chat.whatsapp.com/KFgHYjlqoaUAfjfyxCLDXO Sai mun ji daga gare ku.