Batun yada labaran karya domin cimma manufar siyasa, addini, ko kabilanci abu ne da ya kasance a cikin halayyar dan adam wanda ya samo asali tun lokacin mulkin Rumawa, kamar yadda wasu masana suka bayyana.
Sai dai a baya-bayan nan an sabunta wannan dabi’a domin neman kudi, ba ya ga wadancan dalilai, kuma ta samu karbuwa inda kuma kalmar “Fake News” (Labaran Boge ko na karya) ke neman mamaye kafafen sadarwa na zamani.
Ko ina wannan dabi’ar ta baya-bayan nan ta samo asali?
A tsakiyar shekara ta 2016 ne wani editan shafin Buzzfeed na yada labarai, Craig Silverman, ya lura da wani yanayi na wasu irin labarai da ke fitowa daga wani yanki a wani gari da ke Gabashin Turai.
“Mun lura cewa akwai wasu shafukan Intanet da dama da aka yi musu rajista a wani gari da ake kira Veles a kasar Macedonia,” in ji Silverman.
Shi da abokan aikinsa sun fara bincike bayan zaben shugaban kasar Amurka na shekarar 2016, kuma sun gano kusan shafuka 140 na labaran karya wadanda suna da mabiya da dama a shafin Facebook.
Matasa dai a garin Veles ba su wani damu da siyasa a Amurka ba, amma saboda irin tallan da ake samu a shafin Facebook, shi yasa suke kirkiro da wadannan irin labaran saboda su samu mabiya da dama.
Hakan kuma zai sa su rika samun talla a shafinsu na Facebook.
Zaben shugaban Amurka da kuma takarar Donald Trump sun ja hankalin mutane sosai a shafukan sada zumunta.
Hakan ya sa wadannan mutane a Macedonia suka rika rubuta labaran karya da dama da suka hada da: “Fafaroma Francis yana goyon bayan Donald Trump a takararsa ta Shugaban kasa” da kuma cewa “Jami’in FBI da ya saki sakonnin email din Hillary Clinton ya kashe kansa”.
Wadannan labaran duk labaran boge ne. Wanda kuma daga baya wasu a shafukan intanet suka fara kiransu “Fake News” a Turance wato labaran karya kenan.
Ba sabon abu bane
Yada labaran karya domin cimma wasu bukatu ba wani sabon abu ba ne.
Shekara da shekaru mutane da dama suna yadda abun da ba shi ba ne domin cimma bukatunsu.
- Dabaru 10 na gano ‘labaran karya’
- Me ya sa labaran bogi su ka fi saurin bazuwa?
- Anya Atiku zai iya rage farashin mai kamar yadda PDP ta yi alkawari?
Amma abin da Silverman da abokan aikinsa suka bankado wata dabara ce, ta amfani da labaran karya musamman a shafukan sada zumunta domin samun kudi idan an sanya talla a shafukan saboda zaben shugaban kasar Amurka ya ja hankalin mutane da dama a duniya.
Masu yada labaran karya dai suna nasara ne saboda yadda shafukan sada zumunci suke tasiri, kuma mutane da daman na amincewa da abun da suke karatawa a irin wadannan shafukan saboda dalilai da dama.
Me ya sa ake yada labaran boge?
Bincike da dama da masana suka yi ya nuna cewa mutane kan yada labaran karya ne saboda wasu dalilai da suka hada da wadannan:
Neman kudi: Tsarin da kamfanonin talla a shafukan intanet suke bi domin bayar da talla da kuma tsarin su na bin masu amfani da intanet din a duk shafin da su ke yana taimakawa wurin yada labaran karya.
Domin wannan ne yake sanya wasu mutane su rinka watsa labaran boge domin jan hankalin mutane zuwa shafukansu, wanda hakan zai sa su samu talla daga manyan kamfanoni irinsu Google da Facebook da sauransu.
Wannan ya dace da abin da wadancan matasa na Macedonia da muka ambata tun farko suke yi.
Yada manufa: Wasu kuma kan yi irin wannan aika-aika ne domin yada manufa, wacce kan kasance ta siyasa, addini, ko ta kabilanci.
Irin wannan ya faru a zaben shugaban kasar Amurka na 2016, da kuri’ar raba-gardama ta makomar Birtaniya a Tarayyar Turai, da zaben kasar Indiya na bana.
Haka kuma ana danganta irin wadannan kalamai na karya da rura wutar rikice-rikicen addini da na kabilanci a Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Wasa kwakwalwa: Wasu kuma kan watsa labaran boge ne domin jan hankalin jama’a da kuma wasa kwakwalwa ko nishadantarwa. Wannan ya samo asali tun farkon shigowar rediyo shekaru da dama da suka wuce.
Sai dai har yanzu mutane na ci gaba da yin hakan a shafukan intanet, kuma masana na ganin hakan na da illa domin wasu na daukar wadannan labarai a matsayin na gaskiya.
Bayanai sun nuna cewa shafukan WhatsApp da Facebook da Twitter a nan ne aka fi yada labaran karya a Najeriya.
Sai dai shafin Facebook, wanda har ila yau shi ne ya mallaki WhatsApp ya ce yana aiki tukuru domin shawo kan matsalar. Shi ma Twitter ya ce yana daukar matakai kan batun.
Shin kun ci karo da wani labari, hoto ko bidiyo da ba ku yarda da sahihancinsa ba kuma kuke son a bi muku diddiginsa? Ku turo shi zuwa lambar WhatsApp din shafin http://www.bindiddigi.com +2349027450542 domin a bincika muku sahihancinsa. Za kuma ku iya latsa wannan shafin domin shiga dandalin Ma’abota shafin Bindiddigi a WhatsApp: https://chat.whatsapp.com/KFgHYjlqoaUAfjfyxCLDXO Sai mun ji daga gare ku.