Yunkuri da barazana na baya-bayan nan da kungiyoyin kwadago ke yi a Najeriya na shiga yajin aiki domin gazawar gwamnati kan fara aiki da sabon tsarin albashi mafi karanci na N30,000 na ci gaba da jan hankali a kasar.
An kuma samu cece-kuce da labarai masu cin karo da juna kan yarjejeniya ta baya-bayan nan da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago kan mafi karancin albashi a kasar.
Kungiyoyin kwadago da gwamanatin Shugaba Muhammadu Buhari sun dade suna tattaunawa kan batun tun daga watan Nuwamban bara inda gwamnatin ta yi nasarar shawo kansu suka rage yawan karin albashin da suka bukata daga N56,000 zuwa N30,000.
Sai dai kuma har zuwa yanzu ana fama da bambancin ra’ayi tsakanin bangarorin biyu kan adadin kudin da za a biya a matsayin albashi mafi karanci.
Kungiyar kwadagon dai ta yi nasarar sauya mafi karancin albashi zuwa N18,000 wanda ake biya yanzu bayan ta cimma yarjejeniya tare da gwamnati a shekarar 2010, sannan bayan shekara guda Shugaba Goodluck Jonathan ya sanya wa dokar hannu.
Dokar mafi karancin albashi a Najeriya dai ta tanadi cewa duk bayan shekara biyar za a rika dubawa tare da yin kwaskwarima ga tanade-tanaden dokar.
Akwai yarjejeniya ko babu?
Bayan matsin lamba daga wurin kungiyar kwadago ta NLC gwamanti ta amince ta kafa wani kwamati karkashin jagorancin tsohuwar shugabar ma’aikata ta kasa Ms Ama Pepple da zummar yin aiki da rahoton wani karamin kwamati da aka kafa kafin wannan.
Bangarorin biyu dai sun fara tattaunawa kafin daga baya a samu tsaiko, wanda ya tilasta wa kungiyar kwadagon tafiya wani yajin aiki na gargadi ranar 27 ga watan Satumbar 2018.
An jingine yajin aikin ne kwanaki kadan bayan da gwamnati ta yanke shawarar ci gaba da aikin nemo bakin-zaren.
Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan
- Kungiyar kwadago ta sassauta adadin da ta bukata daga N56,000 zuwa N30,000
- 30 ga Oktoba: Kungiyar gwamnoni ta Najeriya ta yi tayin biyan N22,000.
- 31 ga Oktoba: Kungiyar kwadago ta yi watsi da tayin sannan ta yi barazanar yajin aiki daga ranar 6 ga watan Nuwamba.
- 6 ga Nuwamba: Aka sanar da yarjejeniya tsakanin kwamatin da gwamnati ta kafa da kungiyar kwadago
- 6 ga Nuwamba: Kungiyar kwadago ta dakatar da yajin aikin da ta shirya farawa.
Nawa ne hakikanin adadin mafi karancin albashin da aka amince da shi?
Akwai baki biyu dangane da hakikanin adadin da aka amince na mafi karancin albashin.
Ita dai shugabar kwamatin tana cewa ne sun yi la’akari da bukatar da bangarori biyun suka gabatar; tayin N24,000 daga gwamnati da kuma N30,000 da ‘yan kwadago suka bukata.
An ruwaito ta tana cewa “Babu wata kikikaka”, sannan ta kara da cewa “mun kammala amma mun jaddada musu cewa dole ne a dakatar da yajin aiki. N24,000 da N30,000 su ne adadin da muka bayar”.
A hannu guda kuma kungiyar kwadago ta hakikance cewa N30,000 shi ne abinda aka amince kafin ta dakatar da shiga yajin aikin, wanda daga baya fadar gwamnati ta fitar da sanarwa tana karyata rahotannin cewa Shugaba Buhari ya amince da biyan N30,000 din.

Kungiyar kwadago na son a yi karin albashin kafin zabe
An dai ruwaito shugaban kasar ta bakin mai magana da yawun fadarsa yana cewa “a shirye yake da ya sabunta mafi karancin albashin a nan kusa”, sai dai kuma bai fadi adadi ba.
Su ma gwamnoni daga baya sun bayyana cewa ba sa cikin yarjejeniyar tare da jaddada cewa ba za su iya biyan N30,000 ba sai dai fa idan ‘yan kwadagon sun amince da rage yawan ma’aikata, abinda kungiyar kwadagon ta yi watsi da shi nan take.
Shin zai yiwu a fara aiki da sabon tsarin kafin zabe?
Duk da cewa ‘yan kwadagon sun dade suna fafutika, a bayyane take cewa gwamnati na fuskantar karin matsin lamba musamman saboda karatowar zabe, inda Shugaba Buhari da jam’iyyar APC ke neman wa’adi na biyu.
Kungiyar kwadagon ta kuma bayar da karshen watan Disamba a matsayin wa’adi ga gwamnati na kodai a fara aiki da sabon tsarin ko kuma ta shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani.
Shugaba Buhari a nasa bangaren, shi ma ya yi alkawarin daukar mataki nan ba da jimawa ba don aiwatar da karin albashin, sannan ya bukaci da a kara hakuri.
Sai dai ko da an cimma matsaya, sai an bi wadannan matakan kafin fara aiwatar da sabon tsarin albashin:
- Sai majalisar zartarwa ta amince da shi
- Majalisar tsafaffin shugabannin kasar su ma sai sun amince
- Sai shugaban kasa ya mika daftarin dokar sauyi a mafi karancin albashi zuwa ga majalisun dokoki na tarayya
- Kuma sai ‘yan majalisar sun amince da shi kamar yadda ake yi ga dokokin kasa
- Sannan a mayar wa shugaban kasa ya saka hannu kafin ya zama doka.
Amincewar da duka bangarorin biyu suka yi na cigaba da aiki tare na nuna jajircewarsu duk da cewa har yanzu ba su cimma matsaya kan adadin da za a biya ba.
A hannu guda kuma, ganin yadda ake samun zazzafar adawa daga gwamnoni da kuma matakan da za a bi kafin fara aiki da sabon tsarin albashin, abu ne mai wuya hakan ta faru kafin zaben kasar na watan Fabrerun shekara mai zuwa.
Gwamnati za ta yi kokarin ganin ta fuskanci zaben ba tare da wannan batun ya zamar mata kadangaren-bakin-tulu ba, amma muna ganin cewa ba lallai ne a iya samun nasara ba sai fa idan gwamnati ta yi wani yunkuri na musamman cikin gaggawa.