Mene ne gaskiyar farashin shinkafa a kasuwa da na gwamnati?

See the source image
Jihohin Najeriya da dama sun ce sun dukufa wurin noman shinkafa

A ranar Juma’a 16 ga Nuwamba ne ministar kudi ta Najeriya ta bayyana cewa matakan farfado da tattalin arzikin kasar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dauka sun sa farashin shinkafa ya sauko.

Hajiya Zainab Shamsuna ta shaida wa sashin Hausa na BBC cewa a yanzu ana sayar da “buhun shinkafa a kasar a kan naira 14,500”.

Duk da cewa akwai shinkafa kala-kala a kasar, ministar ta bayyana wannan farashi ne cikin kwarin gwiwa, sannan ta alakanta hakan da nasarorin da ta ce gwamnatinsu ta samu a fannin noma.

Mene ne gaskiyar wannan ikirari na ministar?

Batun farashin shinkafa da sauran kayan abinci dai na daga cikin abubuwan da suka fi ci wa ‘yan kasar tuwo-akwarya, kuma an dade ana jayayya a kan saukin farashinsu ko akasin haka tsakanin gwamnati mai ci da kuma ‘yan adawa.

Su dai ‘yan adawa na zargin gwamnati da lalata tattalin arzikin kasar, yayin da a nata bangaren gwamnatin ke cewa tana kokarin gyara barnar da suka yi a baya ne, abin da ta ce ya jefa kasar cikin matsi.

Image result for zainab ahmed nigeria
Ba a dade da nada Zainab Shamsuna ministar kudi ba

Ko a karshen makon da ya gabata sai da gwamnatin kasar ta ce ta ware naira biliyan 60 domin tallafawa manoma da kuma sauko da farashin shinkafa a kasar, wanda hakan ke kara fito da kalubalen da ake fuskanta.

Nawa ne ainahin farashin shinkafa a kasar?

Mun bi diddigin kalaman na ministar kudi domin gano cewa ko abin da ta fada ya dace da zahirin farashin da talakawa ke sayen shinkafar ko akasin haka.

Bayan tattaunawa da jama’a da kuma ‘yan kasuwa masu sayar da shinkafa a sassan kasar da dama – kudu da arewa, gabas da yamma – mun gano cewa babu tsayayyen farashin shinkafa kamar yadda ministar ta yi ikirari.

Farashin ya shan bambam daga gari zuwa gari, da kuma irin shinkafar da mutum yake son saya domin kowacce farashinta daban.

Akwai wacce ake nomawa a gida da kuma wacce ake shigowa da ita duk da cewa ita ministar kudin bai daya ta yi musu.

Farashin shinkafa kala-kala a wasu sassan Najeriya

A wasu wuraren kamar Kano, shinkafar da ake nomawa a cikin gida ta fi ta waje tsada, wanda hakan ya sabawa ikirarin da ministar ta yi, yayin da a jihar Kebbi, inda cibiya ce ta noman shinkafa, ta gida ta fi ta waje arha, wato kasa da ma farashin da ministar ta fada.

ABUJA

LEGAS KANO ENUGU
14,000 15,000 14,500 14,000
15,000 16,000 15,500 15,500
16,500 17,000 16,000 16,000
17,000 17,500 16,000 16,500

A Abuja babban birnin kasar da kuma jihar Enugu kuwa, shinkafar da ake nomawa a jihar Ebonyi ta Abakaliki Rice ta fi kowacce arha, kuma tana kasa da farashin ministar, yayin da a Legas babu wacce ake sayarwa kasa da farashin da ministar ta bayyana.

Wani dan kasuwa da bai so a bayyana sunasa ba a birnin Kano, ya shaida wa Bindiddigi cewa inganta shinkafar da ake nomawa a gida da kuma kara yawanta a kasuwa zai taimaka wurin saukar farashi domin har yanzu mafi yawan jama’a sun fi gamsuwa da ta waje.

Sakamakon wannan bincike da muka yi, mun fahimci cewa ta wani fannin ikirarin Ministar Kudi Zainab Shamsuna gaskiya ne, yayin da kuma ya kasance ba gaskiya ba ta wani bangaren.

Da alama ko dai ba ta samu cikakkun bayanai game da farashin shinkafa a kasar ba kafin ta yi wancan ikirari, ko kuma ta yi ne domin rudar jama’a.

Ganin yadda batun farashin shinkafar ke da muhimmanci a kasar da kuma yadda zabukan kasa baki daya ke kara karatowa, ya kamata ace duk maganar da jami’an gwamnati za su fada, ta zama gaskiya ce zalla.

Advertisements

Leave a Reply