Akwai wasu sakonni da ake yadawa a kwanan nan a shafukan sadarwa na intanet game da amfani da lambar tantance asusun banki ta BVN da kuma yadda bakuwar fuska kan iya yin amfani da lambar domin ya zambaci mai ita.
Mun bincika lamarin da kuma ta’adi ko zamba da za ta iya faruwa da mutum idan bakuwar fuska ya mallaki lambar ta wani ko wata.
Ga fassarar daya daga cikin irin wadannan sakonnin da aka rika yadawar kamar haka:
“Ina rokonka da kar ka ba wa bakuwar fuska wayarka domin ya yi kira saboda idan ya kira *565*0# zai samu damar ganin lambarka ta BVN sannan kuma zai yi amfani da ita ya zambace ka. Don Allah ka yada wannan sakon domin ka ceci rayuwar wani”.
Me ake nufi da BVN?
- Wasu rukunin lambobi ne guda 11 da ake ba wa masu asusun ajiya a banki
- Tsarin rejistar dai ya kunshi daukar hoton fuskar mai ita
- Cikakken sunan mutum, da adireshi da kuma bayanan ranar haihuwa
- Za a iya amfani da BVN daya ga asusun bankuna sama da daya
- Babban bankin kasa na CBN ne ya kaddamar da shirin a watan Fabreru na 2014
- Manufar shirin shi ne dakile zamba da ayyukan rashin gaskiya a harkar banki.
Me zai faru idan wani ya mallaki BVN dinka?
Wani babban ma’aikacin banki a First Bank Nigeria wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana da ‘yan jaridu ba, ya bayyana wa Bindiddigi cewa mallakar lambar BVN kawai bai isa ya ba wa wani damar zambatar mai ita ba.
Ya ce “Lambar shaida ce kawai da ke dauke da bayanan mutum wadda take makale da asusunsa na banki, sannan kuma mutum ba zai taba iya samun damar mu’amala da asusun ba har sai ya shigar da lambobin sirri (password) ko a Intanet ko a wayar salula ko kuma ta na’urar cirar kudi ta ATM.
Kuma hakan ba mai yiwuwa ba ne ta hanyar kiran *565*0#.”
Masanin ya kuma ce babban hatsarin da ya ke ciki shi ne idan mutumin yana da damar shiga sashen da ke dauke da bayanan BVN na banki, to anan ne za a iya samun bayanai kamar suna da lambar asusu, da bankin da mamallakin BVN din ya yi rijista.
Sai dai kuma wannan damar tana samuwa ne kawai ta hanyar mahukuntan banki ko kuma ma’aikatan kamfanonin haya da ke yin rijistar BVN a madadin wasu bankuna.
Sannan ya kara da cewa “Ko da hakan ta faru babu abin da mutum zai iya yi ya zambace ka ta hanyar taba maka asusun ajiya” sai dai kawai zai iya bayar da bayanan ga bata-gari ko kuma masu talla.
Saboda haka, a yayin da muke karfafa wa jama’a gwiwa kan su kara kaimi wurin kiyaye
bayanansu na sirri, a hannu guda kuma mun gano cewa wannan bayanai da ake yadawa ba su da tushe.
Labaran kanzon-kurege ne da marasa ilimi kan harkokin banki ko kuma wadanda ke neman rikitar da jama’a ke yadawa.