Harin da mayakan Boko Haram suka kai wa sojojin Najeria a jihar Borno, inda suka kashe gwamman sojojin ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar, inda aka rinka musayar yawu tsakanin gwamnati da masu adawa da ita.
Wasu mutane ciki har da wani malamin jami’a mai koyar da aikin jarida da babbar jam’iyyar adawa ta PDP, sun rinka yada wasu hotuna a shafukan sada zumunta da zummar cewa na harin ne. Sai dai hotunan na wani lamari ne da ya faru a wata kasar daban ko ma tsakure daga fina-dinai.
PDP ta fitar da sanarwar Allah-wadai da harin, tare da wallafa wani hoto da ke nuna wasu sojoji da aka kashe, sannan ta ce ya nuna gazawar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wurin yaki da Boko Haram.
Sai dai binciken da muka gudanar ya nuna cewa wannan hoton na dakarun kungiyar Tarayyar Afirka ne da kungiyar al-Shabab ta kasar Somalia ta yi ikirarin kashewa a shekarar 2011.
Mutane da dama ne suka sake yi ta aika wannan hoto a shafin Twitter da Facebook da kuma WhatsApp wanda aka hada da hoton Shugaba Buhari a gefe.
Baya ga PDP wasu masu amfani da shafukan sada zumunta ma sun wallafa irin wadannan hotuna ciki har da Farfesa Farooq Kperogi, wani babban malamin jami’a a Amurka da ke koyar da aikin jarida.
Hoton da ya wallafa ba shi da alaka kwata-kwata da sojojin Najeriya ko kuma rikicin Boko Haram. Hasalima hoton na wani fim din Hausa ne da aka yi a farkon bana.
Daga bisani farfesan, wanda ke da mabiya 20,000 a Twitter, ya amince cewa hoton ba na harin da aka kai wa sojojin Najeriya ba ne bayan da wasu mabiyansa a Twitter suka ja hankalinsa, sai dai bai cire shi daga shafin nasa ba har lokacin da muka wallafa wannan labari.
Farfesa Kperogi dai a baya yana daga na gaba-gaban masu ikirarin kare darajar aikin jarida da jan hankali wajen tabbatar da gaskiyar bayanai kafin a yada su, sai dai a wannan karon da alama mai dokar bacci ya bige da gyangyadi.
Ba ya ga hotuna an kuma rinka yada wani faifan bidiyo da ake ce na harin ne wanda kungiyar Boko Haram ta wallafa, sai dai fitaccen dan jaridar nan da ke da masaniya sosai kan kungiyar, Ahmed Salkida, ya ce bidiyan ba na harin na Maitile ba ne.
Jama’a da dama a shafukan sada zumunta ciki har da jami’an gwamnati da magoya bayanta sun yi Allah-wadai da wallafa wadannan hotuna na karya da labaran bogi game da harin.
A nata bangaren, rundunar sojin Najeriya ta ce tana duba yiwuwar daukar matakan shari’a kan wadanda ta ce sun yada hotuna da labaran karya a kan harin, wanda aka kai a garin Maitile ranar 18 ga watan Nuwamban 2018.
Sai dai babu tabbas ko za ta yi hakan.