Wasu mutane sun rinka yada wannan hoton na dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya Atiku Abubakar yana gaisawa da Shugaban Amurka Donald Trump a shafukan sada zumunta.
Batun ziyarar da ake cewa dan takarar na PDP ya kai Amurka ya kuma samu shiga wasu kafafen yada labaran kasar.
Wani ma’abocin shafin Bindiddigi a Facebook, Sani Haruna ya nemi mu bi diddigin labarin domin tantance shi.
Shekara 13 kenan rabon Atiku Abubakar, wanda ya shahara da yin tafiye-tafiye, da shiga Amurka. Mahukuntar kasar dai ba su bayar da bayani kan dalilan da suka sa ‘aka hanashi’ takardar izinin shiga kasar ba (bisa).
Abokan hamayyarsa na siyasa sun sha nuna cewa rashin zuwansa Amurkar na nufin yana da kashi a gindi. Sai dai ya shida wa BBC a farkon bana cewa ba shi da wani abin boyewa kuma babu wanda ke bincikensa kan wani abu a Amurka.
Me ye gaskiyar labarin?
Wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa dan takarar shugaban kasar ya ziyarci ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, inda aka dauki hoton yatsunsa da tambayoyi irin wadanda ake yi wa masu neman bisa.
Shafin watsa labarai na The Cable ya yi ikirarin cewa Atiku ya samu takardar izinin shiga Amurkar kuma yana shirin tafiya can, yana mai ambato wasu majiyoyi na kusa da shi.
- Babban jami’in APC ya wallafa hotunan boge kan rikicin Boko Haram
- Me zai faru idan wani ya san lambarka ta BVN?
Hoton boge
Binciken da muka yi ya gano cewa hoton da ake yadawa na Atiku yana gaisawa da Trump ba na gaskiya ba ne, hada shi aka yi.
Mr Trump ya kasance a kasar Argentina wurin taron kasashe 20 masu karfin tattalin arziki na G20 a Argentina tun ranar Juma’a, kuma sai ranar Lahadi ya koma birnin Washington.
Mun kuma fahimci cewa Atiku yana birnin Abuja ranar Asabar da yamma, wato 1 ga watan Disamba, bayan ya dawo daga bulaguro zuwa Burtaniya.
Mai magana da yawunsa Paul Ibi ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter:
HE @atiku embarked on a private visit to the United Kingdom on Thursday shortly after the inauguration of his Presidential Campaign Council. He has since returned back to Abuja. #LetsGetNigeriaWorkingAgain
— Paul Ibe (@omonlakiki) December 1, 2018
Ya ce: “Mai girma @Atiku ya yi tafiya zuwa Birtaniya ranar Alhamius jim kadan bayan kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa. Kuma tuni har ya koma Abuja”.
Hoton da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta na soshiyal midiya da ke nuna Atiku yana gaisawa da Trump hada shi aka yi. Binciken da muka yi a shafin Google ya nuna cewa ainihin hoton da aka jirkita an dauke shi ne a shekarar 2017, kuma Pira Ministan Kanada Justin Trudeau ne ke gaisawa da Donald Trump a lokacin da ya kai ziyara fadar White House a shekarar 2017. Ga hoton nan a kasa:
Yunkurinmu na tabbatar da inda aka kwana a batun neman bisarsa ya ci tura domin mun buga wayar Paul Ibe, kakakin Atiku Abubakar, mun tarar da ita a kashe sannan kuma bai amsa sakon da muka tura masa ba har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton.
Mun kuma gwada neman tabbaci a ofishin jakadancin Amurka a Abuja, amma hakar mu ba ta cimma ruwa ba.
A ranar Litinin ne aka tsara cewa Atiku Abubakar zai kaddamar da kamfe dinsa na zaben 2019 a birnin Sokoto.
Biyo bayan binciken da muka yi, mun bayyana labarin tafiyarsa Amurka da hotonsa da Donald Trump da wasu ke yadawa a shafukan sada zumunta da cewa na boge ne.
Shin kun ci karo da wani labari, hoto ko bidiyo da ba ku yarda da sahihancinsa ba kuma kuke son a bi muku diddiginsa? Ku turo shi zuwa lambar WhatsApp din shafin http://www.bindiddigi.com +2349027450542 domin a bincika muku sahihancinsa. Za kuma ku iya latsa wannan shafin domin shiga dandalin Ma’abota shafin Bindiddigi a WhatsApp: https://chat.whatsapp.com/KFgHYjlqoaUAfjfyxCLDXO Sai mun ji daga gare ku.