Wani shafin Facebook mai dauke da sunan “Atiku Abubakar 2019” da ke ikirarin yiwa dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP kamfe a zaben shugaban Najeriya da za a yi shekarar 2019, ya wallafa wani hoton karya na shugaban kasar Amurka Donald Trump yana kiran jama’a da su zabi Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ta PDP.
Shafin dai yana da mabiya fiye da dubu 30 da kuma ya samu masu sha’awarsa wato “likes”” sama da dubu 30. Kuma ya ambato shugaba Trump yana cewa:
“Ku zabi Atiku/Obi domin rage rashin aikin yi, da talauci da kuma habakar tattalin arziki kamar yadda gwamnatimmu ta yi a Amurka. Amurka na sanya a gabana shi ma Atiku Najeriya ya sanya a gaba”.
Sai dai kuma shafin CrossCheck na gamayyar gidajen jaridu a Najeriya domin yaki da labaran boge ya gano cewa hoton na boge ne wanda aka jirkita.
Hoton dai da aka harhada shi ya fara bayyana ne a kafar Intanet a ranar 3 ga Satumba na shekarar 2015 yayinda shi Trump yake nuna goyon baya ga jam’iyyarsa ta Republican a matsayinsa na dan takararta a zaben shugaban kasar da ya lashe.
A bayyane take dai cewa hoton na boge ne kuma an wallafa shi a shafuka da dama na Intanet da wasu sigogin na daban.
Tuni dai mutane da dama suka yada hoton. Bincike kuma ya nuna cewa akwai ire-iren wannan shafi masu dauke da sunan Atiku kimanin 90 wadanda ke yada labaran karya da sunan kamfe ga dan takarar na jamiyyar PDP.
Daya daga cikin irin wadannan shafuka mai dauke da “Atiku Abubakar 2019” ya bukaci mutane da su nemi kyautar Atiku ta hanyar Intanet inda suka kuma wallafa cewa Atikun yana bayar da kyautar Naira dubu 200 ga mutane 500, baya ga sauran batutuwa marasa tushe da shafin ke dauke da su.
Shin kun ci karo da wani labari, hoto ko bidiyo da ba ku yarda da sahihancinsa ba kuma kuke son a bi muku diddiginsa? Ku turo shi zuwa lambar WhatsApp din shafin http://www.bindiddigi.com +2349027450542 domin a bincika muku sahihancinsa. Sai mun ji daga gare ku. Za kuma ku iya latsa wannan shafin domin shiga dandalin Ma’abota shafin Bindiddigi a WhatsApp: https://chat.whatsapp.com/KFgHYjlqoaUAfjfyxCLDXO