
Bincike ya nuna cewa asalin hoton ba shi da alaka da Najeriya
Ana ta yada hoton wani zaki a shafukan sada zumunta da nufin cewa wani
mafarauci ne ya yi nasarar kashe shi a jihar Kogi ta Najeriya.
Sai dai kuma hoton wanda tuni ya karade duniyar Intanet ba shi da alaka da
Najeriya, domin kuwa an gano cewa ya bulla a Intanet din tun a watan Maris na
bana a kasar Angola.
A ranar bakwai ga wannan watan ne wani ma’abocin shafin Facebook ya
wallafa hoto dauke da bayanin cewa: “Wannan jarumin shi ne ya kashe zaki jiya (6 ga Disamba 2018) a garin Ogbonicha.”
Ogbonicha gari ne a jihar Kogi, kuma an yada hoton sau sama da 13,500.
Hatta a shafin Twitter ma an yada hoton inda wasu ke cewa an kashe zakin ne a kasar
Guinea.
A hannu guda kuma, an gano cewa hoton ya fara bayyana a Intanet ne a shafin
Twitter a ranar 11 ga watan Maris inda wani mai suna @Paidalindahotm1 ya saka
da sharhi a harshen kasar Portugal wato Portuguese yana cewa “an kashe zakin
kasar Angola.”
An fara wallafa wannan bincike ne a shafin gamayyar kafafen yada labarai da ke bin kwakkwafin labaran karya ta CrosscheckNigeria.
Shin akwai labaran da kuke so mu tantance? Ku turo mana ta lambarmu ta WhatsApp +234 902 745 0542 ko ta imel a bindiddigi@gmail.com.
Za kuma ku iya shiga dandalin Ma’abota Bindiddigi a WhatsApp domin samun bayanai a kai a kai. Aika sako zuwa (+234 902 745 0542) da bayanin cewa Ina son a saka ni. Ko a latsa wannan shafin: https://chat.whatsapp.com/KFgHYjlqoaUAfjfyxCLDXO