Wasu bayanai da aka yi ta yadawa kwanannan a shafukan Facebook da Intanet sun nuna cewa uwar gidan Shugaba Muhammad Buhari wato Aisha ta umarci ‘yan Najeriya da ka da su sake zabar mijin nata a zaben shugaban kasa a shekarar 2019 mai zuwa.
Wata makala da wani shafin Intanet http://www.exclusive103.com ya wallafa, ya yi kanun labarai da cewa “duk wanda ya sake zabar mai gidana, shashasha ne”.
Sai dai kuma babu wata hujja da take tabbatar da gaskiyar wannan labari.
An yada labarin fiye da sau 22,000 a Facebook kuma jama’a da dama na ci gaba da yada shi.
Sulaiman Haruna mai magana da yawun Aisha Buhari ya shaidawa gamayyar kafofin yada labaran Najeriya masu bin diddigin gaskiyar labarai (CrossCheck Nigeria) cewa uwar gidan shugaban kasar ba ta fadi wadannan kalamai ba, ya kuma kara da cewa akwai zantuttuka iri-iri na boge da ake jingina ma ta a Intanet.
Sai dai makalar ta kuma kunshi wasu ingantattun kalamai na Aisha wadanda ta yi a shafinta na Twitter tun 7 ga watan Oktoba inda take sukar shugabancin jam’iyyar APC, sannan kuma aka gurbata su da na boge.
Wasu makalolin na daban a Intanet sun kunshi wasu kalaman na karya da aka jingina wa ita Uwargidan Shugaba Buharin cewa ta yi barazanar ficewa daga fadar shugaban kasa sannan ta kuma tabbatar da cewa mai gidan nata Buhari ya rasu, wanda kuma mai magana da yawunta ya karyata.
Aisha Buhari ta dade tana sukar gwamnatin mijinta inda ta sha bayyana cewa wasu ‘yan tsiraru ne a fadar shugaban ke tafiyar da gwamantin.
Ta kuma kara da bayyana rashin jin dadinta game da karancin kayan aiki a asibitin fadar shugaban kasa.
Shin kun ci karo da wani labari, hoto ko bidiyo da ba ku yarda da sahihancinsa ba kuma kuke son a bi muku diddiginsa? Ku turo shi zuwa lambar WhatsApp din shafin http://www.bindiddigi.com +2349027450542 domin a bincika muku sahihancinsa. Za kuma ku iya latsa wannan shafin domin shiga dandalin Ma’abota shafin Bindiddigi a WhatsApp: https://chat.whatsapp.com/KFgHYjlqoaUAfjfyxCLDXO Sai mun ji daga gare ku.