Mutane kusan miliyan 10 ne suka kalli wasu hotunan bidiyo a Intanet da suke nuna shahararren mawakin nan marigayi Michael Jackson yana rera wakar “Give Thanks to Allah” a gaban dubban mutane ciki har da tsohon shugaban Amurka Bill Clinton.
Saidai binciken da shafin bin diddigin labarai na kamfanin dillancin labarai na AFP Fact Check ya gudanar, ya nuna cewa bidiyon na boge ne, kuma sautin wakar na asali ya fito ne daga wani mawaki dan kasar Afirka ta Kudu mai suna Zain Bhika https://embed.music.apple.com/us/album/give-thanks-to-allah/397060665?i=397060687 wanda aka hada shi da bidiyon wakar Michael wadda ya gabatar yayin rantsar da tsohon shugaba Bill Clinton na Amurka a shekarar 1993.
A Facebook kadai, mutane kusan miliyan 4 suka kalli bidiyon tun daga watan Fabrairu wadda aka yi wa kanu da cewa: “Kalli da idonka shaharerren mawaki dan Amurka Michael Jackson ya rera wakar ‘Give Thanks to Allah’ a gaban dubban jama’a ciki har da tsohon shugaba Clinton. Ka kalla ka kuma yada, Mun gode”.
An yada wasu samfurin bidiyon a wurare da dama kamar a wannan wallafar a Facebook inda mutane sama da miliyan 2 da dubu dari 2 suka kalla, yayin da a shafin Youtube kuma mutane miliyan 3 da dubu dari 7 suka kalla.
Bidiyon dai ya samo asali ne daga 19 ga watan Janairun shekarar 1993 sa’adda Michael Jackson ya gudanar da wasan dandali a yayin rantsar da tsohon shugaba Bill Clinton, ya kuma rera wakar “Gone too Soon” da kuma “Heal the World”.
Saboda haka ba Michael Jackson ne ya rera wakar “Give Thanks to Allah” ba kamar yadda aka yi ikirari.
Mawaki dan kasar Afirka ta Kudu Zain Bhika shi ne ya rera ta kuma aka makala sautin a jikin bidiyon Michael Jackson.
Shin kun ci karo da wani labari, hoto ko bidiyo da ba ku yarda da sahihancinsa ba kuma kuke son a bi muku diddiginsa? Ku turo shi zuwa lambar WhatsApp din shafin http://www.bindiddigi.com +2349027450542 domin a bincika muku sahihancinsa. Sai mun ji daga gare ku. Za kuma ku iya latsa wannan shafin domin shiga dandalin Ma’abota shafin Bindiddigi a WhatsApp: https://chat.whatsapp.com/KFgHYjlqoaUAfjfyxCLDXO