A ranar 2 ga watan Janairun 2019 da misalin karfe 11:39 wani ma’abocin Twitter mai suna @LadiSpeaks ya wallafa cewa tsohon gwamnan jihar Filato Joshua Dariye wanda ke tsare a gidan yari ya bai wa kwamatin kamfe na shugaba Muhammadu Buhari gudummawar motoci.
A watan Yuni na bara aka yanke wa Dariye hukuncin shekaru 14 a gidan yari bisa laifukan da suka shafi rashawa, inda daga baya kuma aka rage masa zaman kason zuwa shekaru 10.
Jaridar The Cable wadda ake bugawa a Intanet ta ruwaito sakon twitter nasa cewa: “Da dumi-dumi: Tsohon gwamna Dariye wanda ke tsare gidan yari ya bada kyautar motoci samfurin bas-bas guda 25 da tsabar kudi Naira miliyan 50 ga kwamatin kamfe na shugaba Buhari.
“Da alama ‘yan’yan jam’iyyar APC na yin rige-rige ne wurin bai wa kamfe din Buhari gudummawa.”
Mutane dari 747 sun nuna sha’awar sakon an kuma yada shi sau dari 804 sannan kuma aka yi masa martani sau 86.
Mamallakin shafin na twitter ya yi wa kansa lakabi da African giant-Ladi kuma yana dauke da alamar shudi da ke nuna shaidar sahihancin shafin daga mahukuntan Twitter. Sannan ya kira kansa da mamallakin shafin Intanet na @PidginBlogNG kuma kwararre wajen horaswa a shafukan matambayi bay a bata wato Google Digital Skills. Yana kuma da mabiya sama da dubu 62 da 500.
Cibiyar dimokradiyya da ci gaba ta Centre for Democracy and Development wadda ke gudanar da binciken kan labaran karya da ake yadawa a shirye-shiryen zaben Najeriya, ta tuntube shi domin karin bayani, sai dai bai bayar da hoto na motocin ko kuma wata hanya da za a iya tabbatar da sahihancin labarin har zuwa lokacin rubuta rahoton ba.
Daga baya cibiyar ta tuntubi kwamatin kamfe din shugaba Buhari, inda daraktan yada labaran kwamitin Festus Keyamo ya ce ba shi da masaniya ko da gaske an bayar da motocin. Saboda haka ba zai iya tabbatarwa ko karyatawa ba.
“Ba zan iya tabbatarwa ko karyatawa ba saboda ba ni ne shugaban kwamiti ba, sannan kuma ba ni ne mai kula da tsare-tsare ba, irin wadannan gudummawa ofishinsu ake kai wa”, in ji Festus Keyamo.
Israel Ibeleme mai magana ne da yawun Rotimi Amaechi wanda shi ne darakta janar na kamfe din shugaba Buhari, da aka tambaye shi ya ce: “Na yi magana da darakta kuma ya ce babu wata gudummwa daga Dariye. Karya ne.”
Cibiyar ta CDD ta kuma tuntubi mai magana da yawun jam’iyyar APC a jihar Filato kuma ya ce:
“Na tuntubi akalla mutane 3 na kusa da tsohon gwamna Dariye, amma ba wanda ya iya tabbatar da sahihancin labarin, duk sun ce ba su da masaniya. Ina ganin karya ne.”
Cibiyar ta Centre for Democracy and Development ba ta iya tabbatar da ingancin labarin ba ko akasin haka ba, amma duk da haka tana ganin cewa wannan labari na iya zama na kanzon kurege ne maras tushe, domin wanda ya yada labarin ya gaza bayar da shaida da ke nuna cewa an bayar da gudummawar.
Shin akwai labaran da kuke so mu tantance? Ku turo mana ta lambarmu ta WhatsApp +234 902 745 0542 ko ta imel a bindiddigi@gmail.com.
Za kuma ku iya shiga dandalin Ma’abota Bindiddigi a WhatsApp domin samun bayanai a kai a kai.
Aika sako zuwa (+234 902 745 0542) da bayanin cewa Ina son a saka ni. Ko a latsa wannan shafin: https://chat.whatsapp.com/KFgHYjlqoaUAfjfyxCLDXO