Daukar Hoto: Yemisi Adegoke
Kafar yada labarai ta BBC ta kaddamar da wani “gagarumin” shiri na yaki da labaran karya game da zabukan kasa baki daya da za a yi bana a Najeriya.
Shugaban BBC da ke yada labarai ga kasashern duniya, Jamie Angus, ya ce sun dauki matakin ne saboda muhimmancin Najeriya da kuma illar da labaran boge ke haifarwa a kasar da ma duniya baki daya.
Mr. Angus ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taro da BBCn ta shirya a Abuja ranar Laraba 9/1/2019 domin tattuna hanyoyin yaki da labaran karya.
Ana alakanta labaran karya da rura wutar rikicin kablanci da addini a wasu sassan kasar, tare da nuna fargaba kan tasirinsu a zabukan da za a gudanar a Najeriya a watannin Fabrairu da Maris masu zuwa.
Tuni da wasu ‘yan siyasar kasar da magoya bayansu suka fara yada labaran boge kan zaben, inda Shugaba Muhammadu Buhari, da ke neman wa’adi na biyu, ke fuskantar kalubale daga tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar.
Mr Angus ya ce irin wannan fargaba wacce binciken da BBC ta gudanar ya tabbatar, ita ce ta sa su kaddamar da wannan shiri.
“Mu ma kanmu ba mu tsira daga illar labaran boge ba, akwai labarin da sai bayan mun wallafa shi sannan muka gano cewa na boge ne,” a cewarsa.
Abin da shirin ya kunsa
BBC ta za ta rinka samar da bayanai akai-akai domin fayyace gaskiyar bayanai da labaran da ‘yan siyasar Najeriya ke bayarwa a lokacin yakin neman zabe.
Hakazalika shasin kula da intanet na BBC zai rinka bayar da bayanai a harsuna da dama domin wayar da kan jama’a game da labaran karya.
“Za kuma mu rinka samar da horo na musamman ga ma’aikatanmu a Najeriya da sauran sassan Afirka, da kuma abokan huldarmu,” in ji Mr Angus.
Yadda aka kashe ni da raina
Da ya ke jawabi a wurin taron, fitattaccen marubicin nan wanda ya lashe lambar yabo ta Nobel a fannin adabi Farfesa Wole Shoyinka, ya ce labaran karya abu ne na zahiri da ya kamata a tashi tsaye domin a yaka.
“An kashe ni sau da dama a shafukan intanet.”
“Mutane sun sha kira na suna tambaya ko ina da rai, saboda sun gani a intanet cewa na mutu,” in ji shi.
Soyinka ya yi kira ga kafafen sadarwa kamar Facebook da sauransu da su tashi tsaye domin yakar wannan “bala’i”.
Shi ma Mataimakin Shugaban Najeiya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce dole ne kafafen yada labarai su dage-damtse wurin yin binciken kwakwaf domin tabbatar da sahihancin labaran da suke wallafawa.
Ya bayyana yadda wani hotonsa da wasu mata da aka jirkita tare da bayanan boge ya sa matarsa yin korafi da zargin ko ya fara bin matan banza.
Labarin da Mr Osinbajo ya bayar ya sa jama’ar da ke halattar taron, wadanda suka hada da ‘yan siyasa da ‘yan jarida da malaman jami’a, dariya da tafi.