Wani bidiyo da aka wallafa a Facebook ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya ce zai cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar Boko Haram idan ya ci zabe.
Sai dai binciken da sashen bin diddigi na kamfanin dillancin labarai na AFP ya gudanar, ya gano cewa bidiyon na karya ne.
Bidiyon na boge ya yi ikirarin cewa, Atiku zai bai wa Boko Haram wasu garuruwa domin cin gashin kanta hade da wasu rijiyoyin mai a jahar Borno domin a samu zaman lafiya idan ya samu nasara a zabe mai zuwa.
An yi wa bidiyon kanu da cewa “Dole ne mu dakatar da yunkurin Atiku na sadaukar da wani bangare na Borno da rijiyar mai domin samun zaman lafiya. Ku yada wannan bidiyo domin dakile wannan yunkurin rashin tausayin”.
Tuni dai mutum sama da 190,000 suka kalli bidiyon wanda wani shafi mai suna Make Nigeria Worse Again ya wallafa a ranar 8 ga watan Janairu, an kuma yada hotunan da ke cikin bidiyon sau sama da 3,000.
Sai dai a wani bincike da kamfanin dillancin labarai na AFP ya gudanar ya gano cewa, babu wani ikirari mai kama da wannan a cikin kundin manufofin Atiku kuma mai magana da yawunsa Segun Showunmi ya musanta hakan.
A wani sako da ya aike wa AFP, ya ce “Wannan labarin karya ne da ya kamata a hukunta masu yada shi.”
Kamfanin AFP ya kuma gano wani hoto da wani shafi mai suna Naija 24H ya wallafa ranar 6 ga watan Janairu da irin wannan ikirari a Facebook din.
Shin akwai labaran da kuke so mu tantance? Ku turo mana ta lambarmu ta WhatsApp +234 902 745 0542 ko ta imel a bindiddigi@gmail.com