Daga Craig Silverman
Wannan bidiyon da aka hada shi da sabuwar fasahar zamani ta jirkita hutunan bogi da sarrafa su da ake kira “deep fakes” ya na dauke ne da hoton Barrack Obama tsohon shugaban kasar Amurka wanda aka jirkita ta hanyar hada hoton da maganar jarumin fina-finan Hollywood Jordan Peele, wanda hakan ke nuna kwarewar da ake da ita yanzu, da kuma inda aka nufa wajen kirkirar bidiyo da murya da labaran karya.
Bidiyoyi da sautuka na boge irin wadannan na daga cikin matsalolin da za a rika fuskanta a nan gaba. Amma akwai hanyoyi da za a iya bi wajen dakile su.
Hanyoyi na kimiyya da fasaha da ake amfani da su domin yaudarar idanu da kunnuwan mai sauraro na kara samun ci gaba cikin sauri, kamar yadda wani rukunin masana a kasar Jamus ke yunkurin samar da wata manhajar sauya fuska da murya shigen irin wadda aka yi amfani da ita wurin gurbata wannan bidiyon.
Shi ma kamfanin samar da manhajojin jirkita hotuna da muryar na Adobe yana aikin kirkirar manhajar sauya murya, wadda za ta saukaka sarrafa da kuma jirkita maganganun mutane da aka nada, wanda hakan zai ba da damar makala sauti na daban a jikin wani bidiyon na daban na mutumin da ake so a yi wa kazafi, kuma bidiyon ya bayyana kamar na ainihi ba na bogi ba.
An hada bidiyon Obama da Peele ne ta hanyar amfani da da manhajar kyauta ta FakeApp wadda aka samar a baya-bayan nan, kuma mutane da yawa na amfani da ita wurin makala fuskokin taurarin fina-finai a bidiyon batsa.
A kan bata lokaci da kayan aiki masu yawa wurin hada irin wadannan bidiyoyin. Wani kwararre kan hada hotunan bidiyo ya shafe kusan sa’oi 56 wajen hada hoton Obama da magana da kuma motsin bakin Jordan Peele yana Magana, ya hada bidiyon na bogi, wanda ya yi kama da na ainihi.
Sai dai matsalar a nan ita ce, manhajoji irin wadannan suna yaduwa cikin sauri wanda hakan ke bai wa jama’a damar koyansu cikin sauki. Hatta a yanzu da abin ke matakin farko, abu ne mai wuyar gaske banbance tsakanin bidiyo na ainihi, da kuma bidiyon bogi da kwarraru suka yi amfani da fasahohi da manhajoji na zamani irin su Deep Fakes wajen hada su.
Wannan ya sa wasu kwararru suka fara gargadin cewa, mun kusa shiga wani lokaci da zai yi wuya mutum ya iya tantance gaskiyar labarai, hotuna da bidiyo.
Akwai wasu hanyoyi guda biyar da za a iya bi don gane irin wadannan bidiyoyi kamar haka:
1. Hany Farid wani Farfesa ne a bangaren ilimin komfuta kuma ya ba da shawarar kada a yi saurin yanke hukunci zarar an kalli bidiyo har sai an samu karin bayani game da abinda ya kunsa musamman a sabbin labarai.
2. A mayar da hankali kan tushe da asalin inda bidiyon ya fito. Shin shafin da aka saka ko wallafa shi ya kunshi cikakkun bayanai? Wanene ya mallake shi? Daga ina ya samo asali?
3. A jarraba bincika kanun da bidiyon ke dauke da shi a Intanet ko akwai sahihan shafuka da suka ruwaito shi. Kar a yanke hukunci har sai an tuntubi majiyoyi da dama.
4. irin wadannan bidiyoyi na dauke ne da jita-jita, saboda haka sai a saka ido ga bakin mai magana saboda abu ne mai wuya a wasu lokutan a iya hada baki da harshe daidai-wadaida don su dace da murya.
5. Zai yi kyau a kalli bidiyon cikin tsarin tafiyar hawainiya da ma tsayar da wasu bangarorinsa, a kallle su daban-daban domin hakan zai iya taimakawa wajen gano wata tangarda tsakanin hotunan bidiyon.
An fara wallafa wannan makalar ne a jaridar buzzfeed.com
Shin ka ci karo da wani labari da kake tantamar sahihancinsa? Za ka iya aiko mana shi domin tantancewa ta whatsapp a lambarmu +2349027450542. Ko kuma ta adireshin imel bindiddig@gmail.com, da twitter @bindiddigi, da kuma shafimmu na Facebook mai suna Bindiddigi.