Shafin Dailymail da ke Najeriya ya wallafa wani hoto a Facebook, inda yake nuna wani taron siyasa da nufin cewa a Karamar Hukumar Kukawa ne ta Jihar Taraba.
Shafin ya yi ikirarin cewa mutane a wurin sun yi wa dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC korar-kare.
Mutane da dama ne suka yada hoton tun bayan wallafa shi.
Gamayyar ‘yan jaridu ta CrossCheck Nigeria ta tabbatar da cewa labarin na kanzon- kurege ne, domin kuwa hoton na taron yakin neman zaben dan takarar sanata ne na jam’iyyar ADC a mazabar Kogi ta Gabas kwana 10 da suka wuce.
An duba martani da sauran jama’a suka mayar wa shafin, inda aka gano wasu majiyoyin daban, kuma an gano wasu hotunan da suka tabbatar cewa hoton na taron na dan takarar sanatan ne.
Wani shafin Intanet ne mai suna Yes International ya wallafa rahoton a ramar 21 ga watan Janairu kuma ya ce taron sanata ne na ADC wanda “‘yan bangar jam’iyyar APC” suka tarwatsa.
An bincika shafin Facebook na mazabar sanata a jam’iyyar ADC, inda aka ga hoton a cikin wanda wani mai suna Dr. Victor Alewo Adoji 2019 ya wallafa a ranar 21 ga watan Janairu.
Shin akwai labaran da kuke so mu tantance? Ku turo mana ta lambarmu ta WhatsApp +234 902 745 0542 ko ta imel a bindiddigi@gmail.com.
Za kuma ku iya shiga dandalin Ma’abota Bindiddigi a WhatsApp domin samun bayanai a kai a kai. Aika sako zuwa (+234 902 745 0542) da bayanin cewa Ina son a saka ni.