Wasu ma’abota shafukan sada zumunta musamman Whatsapp na ci gaba da yada wani sakamakon zaben gwamnan jihar Ogun na bogi wanda ya nuna cewa ya kamata zaben gwamna a jihar Ogun ya zama ba cikakke ba sabanin abin da hukumar zabe INEC ta bayyana cewa jam’iyyar APC ce ta lashe zabe a jihar.
Bayanan da ake yadawar sun yi ikirarin cewa ratar da ke tsakanin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC da na APM, wadanda su ne kan gaba, ba ta kai yawan kuri’un da aka soke ba, wanda hakan ke nufin zaben bai kammalu ba kamar yadda ta faru a Kano da wasu jihohi.
A tsarin dokar zabe ta Najeriya idan kuri’un da aka soke suka fi yawa a kan na tazarar dan takarar da ya yi nasara ya bayar ga abokan karawar sa, to za a ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba, wato inconclusive a turance.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar a shafukanta na sada zumunta, hukumar zaben Nigeria INEC ta ce Adedapo Abiodun na jam’iyyar APC kuma wanda ya lashe zaben ya samu kuri’a 241,670, inda Akinlade Adekunle Abdulkabir na APM wanda ya zo na biyu ya samu kuri’a 222,153, wanda hakan yake nufin dan takarar APC ya yi nasara ne da tazarar kuri’u dubu 19,517.
INEC din kuma ta ce kuri’u 20,969 ne aka soke sabanin ikirarin masu yada bayanan bogin, wadanda suka ce kuri’u 25,670 ne aka soke, da nufin cewa kuri’un da aka soke sun fi yawa a kan tazarar da dan takarar da ke kan gaba ya bai wa na biyu.
INEC ta ce “an bayyana wanda ya yi nasara ne saboda yawan kuri’un da aka soke ba su kai yawan tazarar kuri’un da aka ci zaben da su ba. Hakan ya dace da sashe na 26 (5) da na 53 (4) na kundin dokar zaben Najeriya ta shekarar 2010, da kuma sakin layi na 33 na kaidojin gudanar da zabe na hukumar zaben.”
Saboda haka ne INEC ta ke jan hankulan jama’a da cewa wannan labarin kanzon kurege ne da wasu ke yadawa domin tayar da fitina da kuma cimma burinsu na kashin kai.