Babu gaskiya a wasu labaran da aka yada cewa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya arce daga kasar bayan hukumar zaben kasar INEC ta sanar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar.
Shi dai tsohon shugaba Obasanjo ya yi bulaguro ne zuwa birnin Landan na Ingila domin ya halarci wani taro da Concordia Africa Initiative ta shirya.
Wani shafi a Facebook mai suna Nija Eye ya wallafa labarin karyar tare da wani bidiyo dauke da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo a wani wuri da ya yi kama da filin jirgin sama.
Wasu shafukan Intanet da dama sun yada bidyon, inda aka kalle shi har sau dubu 160,000, tare da sharhi 262, aka kuma yada shi har sau 7,931 a ranar Juma’a, 1 ga watan Maris da karfe 6:55 na yamma.
Sai dai binciken da gamayyar kafafen yada labarai masu yaki da labaran karya na CrossCheck suka gudanar, ya nuna cewa Cif Olusegun Obasanjo bai fice daga Najeriya ba saboda nasarar da Buhari ya samu, ya fita daga kasar ne don halartar wani taron kasa-da-kasa.
Domin bin diddigin bidiyon, CrossCheck Nigeria ta bincika sunan ‘Obasanjo’ a matsayin maudu’i a shafin Twitter, inda wani bayani ya fito a matsayin sakamako daga shahararren mai amafani da shafin wato @segalink.
Yana cewa ne: “Toyin Saraki wadda ta kafa gidauniyar Wellbeing Foundation Africa ta gabatar da makala a taron Concordia Africa Initiative tare da Cherie Blair da kuma Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Najeriya.”
A ci gaba da binciken ne kuma aka gano cewa tabbas Obasanjo yana halartar taron ne a birnin Landan tare da uwar gidan Bukola Saraki Toyin Sararki.
Da aka tuntubi wani mataimaki na musamman ga tsohon shugaban ya ce hakika Obasanjo ya bar Najeriya zuwa kasar waje amma ya yi hakan ne domin halartar taro, kuma ana sa-ran komawar sa kasar.
Taron na Concordia Africa Initiative an yi shi ne a ranar 28 ga watan Fabarairu, kwana daya bayan sanar da Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu.