Wasu bayanai da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta sun ambato cewa babban bankin Najeriya CBN ya haramta shigar da Atamfofi da yaduka cikin Najeriya daga kasashen waje.
Sai dai duk da cewa CBN din ya sauya dokokinsa game da shigo da Atamfofin a watan Maris na shekrar 2019, sashen bin diddigin labarai na kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya gano cewa, ikirarin cewa an haramta shigo da su baki daya ba gaskiya ba ne.
Shafin Facebook na kamfanin jaridar Nigerian Tribune ya wallafa kanun labari cewa: “Da Dumi-dumi: Babban Bankin kasa CBN ya haramta shigowa da atamfofi da yaduka”
Kanun labaran dai yana dauke ne da wani adireshi da ke iya kai mutum zuwa ga wata makala a shafin Intanet na jaridar Nigerian Tribune. Makalar wadda ta kunshi sakin layi hudu ba ta yi wani gamsasshen bayani ba game da haramcin da aka yi ikirari a kanun labarin ba.
A madadin haka, makalar ta yi bayananin cewa CBN ya ayyana atamfofi da yadukan wato textiles a jerin kayayyakin da bankin ba zai basu damar amfana daga tsarinsa na bayar da canjin kudaden kasar waje domin shigo da kaya Najeriya ba, wanda hakan ya dace da dokokin bankin.
Hakan yana nufin duk dan kasuwar da zai yi safarar atamfofi da yadukan, to sai dai ya sayi dalar Amurka da sauran kudaden kasar waje a kasuwar bayan fage, ba a hannun bankuna ba da kuma sauran cibiyoyi na hukuma.
Ana sayar da dala daya a kan N305 bisa farashin bankin CBN tare da yin sauki ga mai saya da kuma masu sayan Naira don zuba jari a Najeriya. A kasuwar bayan fage kuwa ana sayar da ita ne a kan N360.
Bankin CBN ya fara kayyade adadin kudaden musayar da ‘yan kasa za su iya samu daga bankuna ne tun bayan da aka samu faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya, wanda ta nan ne Najeriya ke samun mafi yawan kudaden kasar wajen.
Babban bankin ya kuma lissafa wasu kayyayki 41 wadanda ba za su samu dala ba a hannunsa. Kayayyaykin sun hada da tsinken sakace, shinkafa, siminti da kuma turaren wuta kirar kasar Indiya. Wannnan, in ji bankin, zai taimaka wajen habaka kayan da ake sarrafawa a cikin gida da kuma adana kudaden kasar wajen.
CBN ya kara da cewa duk dan kasuwar da yake so ya ci gaba da shigo da wadannan kayayyaki to zai iya ci gaba domin bai haramta ba, kawai dai ba zai samu canjin dala ba a farashin hukuma.
Mene ne ya canza game da dokar shigo da Atamfofi da yaduka?
A ranar 5 ga watan Maris Gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya fada a wani taro na masu noman auduga cewa, CBN ya sanya atamfofi da yaduka a jerin kayan da gwamnati za ta daina sayar wa da ‘yan kasuwarsu dala a farashin hukuma.
Mai magana da yawun Gwamnan CBN Isaac Okorafor ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “sanarwar da gwamnan ya bayar ba ta nufin haramci game da shigo da atamfofi da yadukan”.
Isaac Okorafor ya ce “kawai dai an haramta sayar da kudaden kasar waje ne a farashin gwamnati ga duk wanda ke son shigo da kayan cikin Najeriya daga kasar waje”.