Wasu bayanai da aka yada a shafukan sada zumunta wanda kuma wasu jaridun Najeriya suka wallafa rahotanni a kansu sun yi ikirarin cewa Aliyu Sani, wani magoyin bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya mutu bayan ya sha ruwan kwata domin murnar lashe zaben da shugaban ya yi.
Babu gaskiya game da zancen mutuwar tasa, domin kuwa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya yi hira das hi a ranar 22 ga watan Maris.
Jim kadan bayan an bayyana Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabarairu, hoton wani mutum da aka bayyana a matsayin Bala Haruna ya karade kafar Intanet.
Mutumin daga garin Bauchi, an ce ya shiga cikin kwata tare da shan ruwanta duk domin nuna farin cikinsa ga nasarar da Buhari ya yi ta lashe zaben a karo na biyu.
Wata shahararriyar marubuciya a kafar Intanet Linda Ikeji da kuma jaridar Legit da ake bugawa a Intanet suna cikin wadanda suka fara buga labarin.
‘Yan kwanaki kadan sai wani shafin Twitter mai suna “NaijaVirals” ya kuma wallafa hoton da kanun cewa: “Bala wanda ya yi alwashin shan ruwan kwata idan Buhari ya yi nasara ya mutu bayan an garzaya da shi asibiti sakamakon ciwon ciki”.
Jaridar The Guardian ita ma ta wallafa irin wannan ikirari wanda wani Sanata a Majalisar Dattawan Najeriya Murray-Bruce ya yada a shafinsa na Facebook da Twitter.
Sunana Mohammed Sani kuma ina raye ban mutu ba
Ali Gayu kenan yana nuna wa AFP kwatar da ya shiga kuma ya sha ruwanta don murnar cin zaben shugaba Buhari
Kamfanin dillamcin labarai na AFP ya bi diddigin mutumin kuma ya gano cewa sunansa Ali Mohammed Sani wanda ake masa lakabi da Ali Gayu. Yana da shekara 23 kuma yana zaune a Unguwar Doya a garin Bauchi.
Ali Mohammed ya ce shi bai kamu da wani ciwo ba banda dan zafi da ya ji a idanunsa, kuma bayan kwana biyu suka daina.
“Na yi sa’a cikin kwana biyu idanuna suka daina zafi kuma suka washe sabanin abin da na ji ana fada cewa ciwon ciki ne ya yi sanadiyyar mutuwata”, in ji Ali Gayu.