Wani shafin yada labarai da Hausa mai suna Arewa Dailypost ya yada wani hoto wanda ya yi ikirarin cewa na gawarwaki ne da aka kashe a wani hari da aka kai a ranar Juma’a a yankin Maradun na jihar Zamfaran Najeriya.
Sai dai binciken da shafin Bindiddigi ya gudanar ya gano cewa, hoton ba na harin Maradun ba ne.
Wani ma’abocin Bindiddigi mai suna Yarima Hassan ne ya ci karo da labarin kuma ya jawo hankalin Bindiddigi domin tabbatar da sahihancin hoton ko akasin haka.
Hoton dai kamar yadda muka gano ya bayyana a Intanet tun a ranar 22 ga watan Maris na shekarar 2017 a wani dandalin muhawara mai suna Nairaland, inda aka ce gawarwakin wasu ‘yan kasuwa ne da suka yi hadari a jihar Kebbi.
Hoton ya kuma bayyana a shafin publicvoice.ng a watan Afrilu na shekarar 2017.
Tuni dai mutane sama da dubu 1 suka nuna sha’awarsu wato ‘like’ ga hoton inda aka kuma yada shi sau fiye da dubu 1 da 400.
Hakan na dada nuna yadda bayanan karya ke yaduwa kamar wutar daji.
Rawar da jama’a ke takawa wajen dakile labarun karya
A wallafar da shafin na Arewa DailyPost ya yi a Facebook mutane da dama sun jawo hankalinsa cewa hoton da ya wallafa ba na harin Maradun ba ne, amma ya hakikance cewa na harin garin Maradun din ne.
Wani mai suna Isah Albani ya yi martani da cewa: “Ya kamata gidajen jaridu su dinga kiyayewa akan wallafa duk abinda ba daidai ba.”.
Kareema Ahmad Rufai kuwa cewa ta yi “Wannan gawarwakin wasu ‘yan kasuwa ne da suka yi hadari kwanakin baya.”