
Labaran kanzon-kurege sun shigewa jama’a da dama a duniya hanci
Batun yada labaran karya ko kanzon-kurege na ci gaban da jan hankalin jama’a musamman masu amfani da shafukan sada zumunta.
Wannan batu dai ya zama ruwan-dare kusan a duk fadin duniya, inda kuma za a iya cewa ya shafi kowa da kowa.
Ga wasu abubuwa hudu da za su taimaka wurin yakar wannan dabi’a ta yada labaran boge – daya-daya ga ‘yan siyasa, shafukan sada zumunta, ‘yan jarida da kuma jama’ar gari – kamar yadda shafin Axios ya wallafa.
‘Yan siyasa
Ku daina amfani da kalmar “Fake news – wato labaran karya”. Abu mafi muni ga kasa shi ne jama’arta su rinka amincewa da labaran karya ko kuma su ki amincewa da kowanne irin labari.
Wata rana wani mummunan abu zai faru, kuma dole sai an bukaci amincewa da kafafen samar da bayanai kafin a shawo kan batun. A don haka yin kafar-angulu ga wannan fanni kamar yi wa kai ne.

Donald Trump yana yawan amfani da kalmar “labaran karya” ga labaran da ba su yi masa dadi ba
Kafafen yada labarai
Ya kamata su haramtawa ma’aikatansu yin komai a shafukan sada zumunta – musamman Twitter – idan ba wallafa labarai ba.
Wasa, barkwanci da bayyana ra’ayi ba nasu ba ne, domin yana sawa ana gane inda suka karkata, kuma zai yi wuya su iya gamsar da masu sabanin ra’ayi irin nasu daga baya.
Shafukan sada zumunta
Ya kamata su kafawa kansu tsauraran ka’idoji ko kuma su bar gwamnati ta kafa musu domin shawo kan kwararar labaran kanzon-kurege da rudani.
Ya kamata su rinka bin ka’idoji kamar yadda gidajen talbijin da rediyo ke bi. Abin da ya fito fili shi ne wannan tsarin da ake amfani da shi yanzu ba ya tasiri.
Sai kai kuma
Dan adam na son dora laifi kan wani amma a zahiri dukkanmu muna da laifi. Watsawa ko tura labarai ba tare da an karanta su ba.
Wallafa duk wata damuwa a shafin Twitter. Latsa duk wani shirme da aka wallafa. Mai zai hana ka dan dauki lokaci kalilan domin tantance gaskiyar abin da ka/ki ka karanta.
Ya kamata a fahimci cewa idan shafinka/ki na Facebook ya cika da labaran kanzon-kurege to babu shakka su za a ci gaba da turo maka domin na’urar da ke lura da halayyar kwamfiyuta abin da ta sani kenan game da kai/ke.