Wani shafin Facebook na boge na wallafa wasu jerin bayanan karya kan zaben da za a sake a wasu mazabu a jihar Kano ta arewacin Najeriya.
Shafin, wanda aka yi wa lakabi da “Bbc hausa nigeria” na yin wadannan bayanai da sunan kafar yada labarai ta BBC Hausa, wacce jama’a ke matukar martabawa kuma suka aminta da labaranta.
Daga cikin labaran bogen da wannan shafi ya wallafa sun hada da ikirarin cewa tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar PDP a jihar, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce zai rushe dukkan masallatan da gamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta gina idan PDP ta ci zabe.
Har ila yau sun wallafa wasu labaran na karya makamantan wannan.
Sai dai binciken da muka gudanar ya gano cewa wadannan labarai na karya ne kuma ba su da asali saboda dalilai kamar haka:
- Wannan shafi ba na BBC ba ne, an kirkire shi ne domin rikitar da mutane da yada labaran karya
- Shafin BBC Hausa na dauke da alamar shudi wacce ke nuna cewa ingantaccen shafi ne. Sannan kuma za a ga an rubuta “BBC News Hausa”, kuma yana da mabiya sama da miliyan biyu.
- Duk da cewa Sanata Kwankwaso ya yi hira da BBC wacce aka watsa a ranar Asabar 16/03/2019, babu inda batun ginawa ko rushe masallaci ya fito a cikin hirar.
- Tuni Sanata Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na Twitter yana zargin masu hamayya da shi da yunkurin bata masa suna ta hanyar amfani da wasu kafafen yada labarai.
- Mun bincika duk wasu kafafen yada labarai masu inganci a ciki da wajen Kano amma ba mu ga inda aka bada irin wannan rahoto ba.
A ranar Asabar ne za a gudanar karashen zaben gwamna na jihar Kano, inda jam’iyyar PDP da APC za su fafata a wasu mazabu domin tabbatar da wanda ya yi nasara.
Don haka jama’a sai a yi hattara da masu yada labaran karya.
Idan ba ku gamsu da labari ba za ku iya turo mana shi domin mu bi diddigi mu tantance muku.
Sai ku turo mana ta lambarmu ta WhatsApp +234 902 745 0542 ko ta imel a bindiddigi@gmail.com.
Za kuma ku iya shiga dandalin Ma’abota Bindiddigi a WhatsApp domin samun bayanai a kai a kai. Aika sako zuwa (+234 902 745 0542) da bayanin cewa Ina son a saka ni. Ko a latsa wannan shafin