
Emmanuel Macron na da kyakkyawar alaka da shugaban Najeriya
Wata makala da aka yada sau sama da 1,500 a shafin Facebook ta yi ikirarin cewa Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana goyon bayansa ga samar da kasar Biafra a Najeriya.
A cewar bayanin, Shugaba Macron ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, inda ya kira Biafra a matsayin “zuciyar Afirka”, in ji makalar.
Sai dai a wani bincike da sashen bindiddigin labarai na kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya gudanar ya gano cewa labarin ba shi da tushe, Macron bai yi wannan magana ba a Twitter ko a wani wuri na daban.
A cikin makalar da aka wallafa a shafin Intanet mai suna The Pointer News a ranar 29 ga watan Disambar 2018 an yi ikirarin cewa shugaban Faransar ya yi kira ga shugabannin Afirka a Twitter a ranar 25 ga watan Disamba da su goyi bayan Biafra:
“Ina kira ga shugabannin Afirka gaba daya da su mike tsaye domin tabbatar da nasarar kafuwar kasar Biafra kafin matsalar ta gagari kundila”.
Yunkurin kafa kasar Biafra dai ya fara ne tun a shekarar 1967 wanda ya jawo mummunan yakin basasa a Najeriya na tsawon wata 30, inda mutum sama da miliyan daya suka rasu mafi, yawansu al’ummar Igbo.
AFP ya bincika shafin Twitter na Emannuel Macron kuma ya gano cewa bayani guda daya da aka wallafa a shafin nasa a 25 ga watan Disamba na murnar Kirsimeti ne wanda ya yi shi da matarsa Brigitte.
Ma’aikatar harkokin kasashen waje a birnin Faris ta tabbatar wa da AFP cewa Shugaban bai yi wannan kalami ba a kafafen sada zumunta ko kuma a fili.
Suka ce: “Muna musanta wadannan kalamai da ake dangantawa ga Emannuel Macron. Babu wani zance mai kama da hakan a Twitter da ya yi.”
Tuni dai Shugaba Muhammdu Buhari ya ayyana kungiyar masu fafutikar kafa jamhuriyar Biafra ta IPOB a matsayin “‘yan ta’adda”, kuma shugabanta Nnamdi Kanu, wanda ya tserewa beli, yana fuskantar shari’a kan cin amanar kasa.