Wasu hotunan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta dauke da wasu sakonnin talla like a jikin manyan motocin bas a birnin Landan wadanda ke kira da a garkame Bukola Saraki a gidan yari ba na gaskiya ba ne.
Binciken da sashen bin diddigin labarai na kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya gudanar, ya nuna cewa hotunan bidiyon, wadanda aka kalla sau sama da 130,000 a dandalin Facebook, da Instagram, da kuma YouTube na boge ne, kuma an yi amfani da fasahar kirkira ko jirkita hotuna wajen lika kalaman – da ke kiran a garkame saraki – a jikin motocin.
Bidiyon farko dai ya bulla ne ta wani shafin Facebook mai suna Kwarans wadda aka yada shi sau 8,600, inda kuma aka kalle shi akalla sau 109,000 tun lokacin da aka wallafa shi a ranar 11 ga watan Maris na 2019 tare da kanun: “Motoci dauke da kiran a kulle Bukola Saraki sun bulla a titunan Landan”
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ci gaba da bin diddigin shafin kuma ya gano cewa shafin ya samu sababbin mabiya sama da 1,500 tun bayan da ya wallafa bidiyon. Shafuka daban-daban sun yada bidiyon a Instagram da kuma YouTube, har ma da Twitter.
Bidiyo na biyu da shafin Kwarans ya wallafa, shi ma wani shafi mai suna Goldmyne TV da ke dauke da alamar sahihanci daga twitter ya yada shi a dandalin Instagram. Shafin yana dauke da mabiya sama da 900,000.
Da gaske kamfanin motocin safara na Landan na karbar talla?
Duk da cewa kamfanin motocin safa-safa na Landon wato Transport for London, wanda ke kula da zirga-zirgar manyan motocin bas din yana karbar talla sai dai abu ne mawuyaci wannan tallan ya zama sahihi, domin kuwa kamfanin ba ya karbar tallan siyasa. Za a iya karanta ka’idoji da tsarin kamfanin a nan.
Da kamfanin labarai na AFP ya tambayi kamfanin ko yana da masaniyar wannan tallan da ke yawo a jikin motocinsa? Kamfanin ya amsa da cewa: “wannan tallan na kage ne”.
A lokuta da dama akan gane bidiyon asali wadda aka gurbata, sai dai a wannan karon hakan ya ci tura, domin kuwa shafukan bankado bidiyon karya kamar InVid bai iya ganowa ba. Babu mamaki wanda ya hada bidiyon ya dauki bidiyon ne da kansa a birnin London.
Duk da haka, kana kallon bidiyon za ka lura cewa gurbin da aka rubuta tallan ya fita daban da sauran sassan bidiyon, domin kuwa ya fi haske sosai. A bayyane yake cewa akwai manhajoji iri-iri da ake iya amfani da su don lika harufa a jikin abu mai motsi a cikin bidiyo.
Magoya bayan jam’iyya mai mulki ta APC a Najeriya na ta yin kiraye-kirayen a gurfanar da Bukola Saraki a gaban kotu bisa zargin aikata lefukan rashawa, tun bayan da ya bar jam’iyyar zuwa jam’iyyar adawa ta PDP kafin babban zaben kasar na watan Fabarairu da ya gabata.