Sa’o’i 24 bayan kammala kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya a Najeriya, an samu sakamako na boge kala-kala da mutane suka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta.
Sakwanni da dama ne aka yada har sau sama da 30,000 a Twitter da Facebook wadanda ke bai wa ‘yan takarar da suka fadi nasara, ko kuma bai wa wadanda suka yi nasara faduwa, kamar yadda rahoton da sashen bin diddigin labaran karya na kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya wallafa.
Wasu bayanan kuma sun yi kokarin kara gishiri a miya ne don kara nuna farin jinin dan takararsu. Sai dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ita kadai ce aka bai wa damar sanar da sakamakon zabe a Najeriya.
Ana sanar da sakamakon zaben‘yan majalisar kasa ne a matakin jihohi daga bakin turawan zaben da INEC ta tura jihohin, sannan kuma shugaban INEC din na kasa shi ne ke da alhakin sanar da sakamakon shugaban kasa da kuma wanda ya yi nasara.
Misalan sakamakon karya
An yada wani sakamako da shafin Scannews ya wallafa a Facebook sau sama da 2,800, wanda ya yi ikirarin cewa shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Sararki ya lashe zaben mazabar jihar Kwara ta Tsakiya.
Sun saka hoton Saraki tare da kanu cewa: “Mai Girma Saraki ya yi nasarar lashe kujerarsa, PDP = 211,591 APC = 82,642”. Wannan ba gaskiya ba ne, a sakamakon da baturen zaben jihar Kwara ya sanar ya nuna cewa Saraki ya fadi.
Wani shafin kuma mai suna Dailymail gist, shi ma ya wallafa labarin, kuma an yada shi sau sama da 2,400.
Kazalika, wani mai sharhi kuma magoyin bayan jam’iyyar APC ya bayyana cewa Saraki ya fadi, amma sai dai ya kara yawan kuri’un da abokin takararsa na APC ya samu sama da hakikanin abinda ya samu.
A sakamakon da INEC ta fitar a jihar, Saraki ya samu kuri’a 68,994, inda dan takarar APC ya kayar da shi da kuri’a 123,808.
Buhari na nasara Atiku na nasara
Tun kafin hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a hukumance, kamar yadda dokokin Najeriya suka tanada, magoya bayan manyan ‘yan takarar shugaban kasa guda biyu sun yi ta ikirarin cewa jam’iyyunsu ne suka yi nasara.
Femi Fani-Kayode tsohon ministan sufurin jiragen sama ne kuma jigo a jam’iyyar PDP, ya yi ikirarin cewa Atiku ya doke Shugaba Muhammadu Buhari, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook.
Dan jam’iyyar adawa Demola Olarewaju ya fada a Twitter cewa: “Atiku ya lashe wannan zaben. Buhari ya fadi a Abuja, inda ya samu kashi 23% kawai.”
Su ma magoya bayan Buhari sun yi ikirarin nasara tun kafin a sanar da sakamakon zabe, ciki har da mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan kafafen yada labarai na zamani Bashir Ahmad.
Daga bisani dai hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar da cewa, Shugaba Muhammad Buhari na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben.
Yayinda ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a Najeriyar, ga wasu bayanai kan yadda za a gane sakamkon boge idan an yada shi:
Wanene yake yada shi?
Domin tantance sakamakon boge, da farko ka san jam’iyyarbangaren siyasar da wanda ya wallafa sakamakon yake goyon baya. Idan yana goyon bayan jam’iyyar da aka ce ta yi nasara ne a sakamakon da aka yada, to sai ka nemi sanin majiyarsa.
Mecece majiyar?
Shin an jingina sakamakon ga wata majiya mai tushe? Jarida ce? Ko baturen zabe ne? Za ka iya gano wasu sahihan majiyoyin daban?
Me ingantattun kafafen yada labarai na cikin gida ke cewa a kai?
Ingantattun kafafen yada labarai na cikin gida suna da wakilai a sassa da yawa na kasa, har da cibiyar tattara sakamako wadanda suke aikewa sakamakon kai-tsaye a lokacin da ake sanar da shi.
Idan ka ga sakamako a kafar sada zumunta ka duba kafafen yada labarai na cikin gida. Idan sakamakon ya yi daidai to akwai kanshin gaskiya a sakamakon.
Shin INEC ta fadi sakamakon?
Tambayar karshe da za ka yi ita ce: mene ne matsayin hukumar zabe? Idan INEC ba ta sanar da sakamakon a fili ba, to ba za a ce sakamakon ya tabbata a hukumance ba.