Bayanai sun nuna cewa ikirarin Atiku na cewa labarin ba da kwangilar na “karya” ne ba gaskiya ba ne.
Yunkurin dan takarar jam’iyar PDP na Najeriya, Atiku Abubakar domin samun goyon bayan kasar Amurka ta ayyana shi a matsayin halattaccen zababben shugaban kasa a babban zaben da ya gabata a kasar bai tsaya a kalubalantar zaben bisa turbar shari’a ta cikin gida ba.
Atiku da PDP sun himmatu wajen kasha makudan kudade domin samun tagomashin goyon baya daga gwamnatin Amurka.
Sai dai bayanai sun nuna cewa ikirarin da Atiku Abubakar yayi na cewa “karya ce tsagwaronta” batun bayar da wangilar aikin tabbatar da shi a matsayin halattacen zababben shugaban Najeria ba gaskiya bane.
A wani kundi da kafar yada labarai ta ICIR ta samu mai lamba 6654, an bayyana yadda Atiku Abubakar ya dauki hayar Fein & Delvalle PLLC – wani kamfanin kwararrun lauyoyi da ke birnin Washington DC.
Ya nemi kamfanin ya yada manufa da zummar samun goyon bayan majalisar kasar Amurka da kuma gwamnatin kasar akan watsi da sakamakon zaben da hukumar INEC ta bayyana, har sai kotu ta kamala sauraren korafin zaben da Atikun ya shigar a gabanta na kalubalantar nasarar Shugaba Buhari.
Aikin kwangilar zai lamushe dalar Amurka $30,000 domin biyan hayar ofis, zirga- zirgar cikin gida da sauran dawainiya kuma za a kamala aikin cikin kwanaki 90.
Kasar ta Amurka dai ta riga ta taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar sake lashe zabe jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben.
Hakazalika, mako daya da kammala zaben ne aka ruwaito sakataren harkokin kasashen wajenta Mike Pompeo ya fitar da wata sanarwar cewa zaben na Najeriya ingantacce ne.
Pompeo, ya kara da jaddada goyon bayansa ga ingancin zaben wanda rahotannin masu sanya idanu na ciki da wajen Najeriya suka ayyana a matsayin ingantacce.
Aikin na Fein & Delvalle ya hada da tuntubar mambobin majalisar wakilai da ta dattijan kasar domin amincewa akan wani kuduri da zai jingine ayyana wanda ya yi nasara a zaben na Najeriya har sai an kamala saurarar karar da Atiku ya shigar.
Haka nan, aikin ya kunshi rubuta wata kasida da za ta yi tsokaci akan al’amuran bayan zabe da nufin haska muhimmancin mutunta dokokin kasa, bin ka’idar aiki wajen warware takaddamar bayan zabe a Najeriya.
Daga karshe kuma kamfanin zai shirya tallace-tallace da jan hankali a kafafen talabijin da sauran hanyoyin sadarwa domin jan ra’ayin jama’a akan al’amarin.
Dadin-dadawa, an nakalto cikin wata takarda yadda kamfanin na Fein & Delvalle PLLC ya bayyanawa Atiku Abubakar cewa “Zai shirya dakin tattara bayanai a ofishinsa na Capitol Hill dake Lamba 300 a lungun New Jersey, NW, Suite 900 a birnin Washinton DC”.
Wani lauya dan Najeriya kuma na hannun daman Dr. Lloyd Ukwu shi ne aka zaba domin taimakawa wurin gudanar da dakin tattara bayanai ta hanyar basu karin haske daga cikin gida Najeriya.
Kamfanin ya kuma amince akan gamsar da kasar Amurka cewa Atiku Abubakar zai gabatar da gwamnati budaddiya a tarihin mulkin Najeriya wacce za ta tafi da kowa ba tare da wariyar addini, kabila ko bangaranci ba.
Haka kuma za ta tabbatar da daidaito, adalci da ‘yanci ga kowa tare da bin ka’ida.
Kwangilar farko ta dala miliyan daya ($1m) tun bayan kammala babban zaben 2019, an ruwaito jerin kwantiragi uku ne Atiku Abubakar ya bayar ga kamfanoni na kwararrun lauyoyi masu shawo kai na kasar Amurka domin cimma burinsa.
A watan Satumba, jamiyar PDP, a madadin dan takararta na shugaban kasa ta
sanya hannu a kwantiragin shekara daya da Ballard Partners – wani sanannen kamfanin masu shawo kai a Amurka domin gamsar da kasar ta goyawa Atiku baya.
Takardar yarjejeniyar ta ce “Aikin kamfanin ne tuntubar wadanda suka bashi aiki tare da jan hankalin gwamnatin Amurka bisa wasu al’amura da ke tattare da zaben na 2019.
Kunshin takardar ya kara da cewa “Manufar kwantiragin zai hada da inganta alakar Amurka da Najeriya, kyautata tsarin dimokaradiyya a Najeriya.
Ana kyautata zaton cewa aikin na kamfanin shi ne ya kawo karshen haramtawa Atiku Abubakar shiga Amurka ta yadda gwamnatin kasar ta dage haramcin bisa ayyukan kamfanin.