Bincike ya nuna cewa bidiyon na shekarar 2013 ne kuma ba a kan Buhari gwamna el-Rufa’i ke magana ba.
Dubban mutane ne suka yada wani bidiyo da ke dauke da hoton gwaman jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufai yana maganar cewa Shugaba Muhammadu Buhari yana da masaniya kan wadanda ke kai hara-hare a jihar Zamfara.
Sai dai bidiyon an wallafa shi don kawai a zambaci mutane ne, domin an yi hirar ne da el-Rufai tun a shekarar 2013 kafin Buhari ya zama shugaban kasa, kuma ma ba a kan Zamfara yake magana ba.
An yada wani bangare na bidiyon sama da 5,500 a Facebook, wadda aka wallafa ranar 8 ga watan Afrilu tare da kanun cewa: “Jami’an tsaro sun bai wa Buhari rahoto kan ‘yan bindiga da kuma Boko Haram da wadanda ke daukar nauyinsu don ya dauki mataki – El-Rufai”.
Shafin Scannews, wanda ya kware wajen yada labaran karya a Facebook ya wallafa bidiyon, inda shi kuma yake nuna cewa el-Rufai yana magana ne kan Shugaba Buhari da kuma kasha-kashe a Zamfara.
- Shin Osinbajo ya fadi gaskiya kan saukar farashin taki zuwa 5,500?
- Kure-karya: Kwankwaso bai ce zai rushe masallatai ba
An yada bidiyon da suka wallafa sama da sau dubu.
A shafin Intanet na Nairaland da Naijaloaded ma an wallafa bidiyon, wadanda suke cikin dandalin muhawara na Intanet da aka fi ziyarta a Najeriya.
Boko Haram
“Mun yi amfani da karfin soja muna tunanin za mu kawo karshen abin, wannan ba mai yiwuwa ba ne.
Na dade a cikin gwamnati kuma na samu rahotannin tsaro masu yawa a matsayina na minister,” el-Rufai ya fada a bidiyon.
Ya kara da cewa “Shugaban kasa yana samun ninki 50 na irin wadannan rahotanni. Na kalubalanci shugaban hukumar DSS cewa sun san wadannan ‘yan bindiga. Shugaban kasa ma ya san su.”
Idan aka jirkita zancen, cikin sauki za a iya fahimtar cewa el-Rufai yana magana ne kan Buhari da kuma kasha-kashen baya-bayan nan da ake fama da shi a jihar Zamfara.
A kashin gaskiya dai, bidiyon tana nuna el-Rufai ne a wata hira da aka yi da shi a shirin STRAIGHTalk na kafar talabijin ta TVC, wadda kuma aka wallafa a shafin YouTube a watan Mayun 2013.
Kuma yana magana ne kan tsohon Shugaba Goodluck Jonathan game da rikicin Boko Haram, wanda dama shi ne maudu’in hirar.