A 2016 mutum 42,430 ne suka bayyana kansu a matsayin ‘yan ci-rani daga Najeriya a kasar ta Canada.
Wata makala da aka yada sau sama da 3,000 a Facebook da Twitter ta yi ikirarin cewa Firaministan kasar Canada Justin Trudeau ya roki Shugaba Muhammadu Buhari da ya tura ‘yan ci-rani miliyan daya daga Najeriya zuwa kasarsa.
Wannan ba gaskiya ba ne, domin ofishin jakadancin kasar a Najeriya ya musanta labarin, amma ya ce ‘yan Najeriya za su iya neman izinin shiga kasar ta hanyoyin da suka dace.
Makalar wadda wani shafin Intanet CBTV ya wallafa, ta ce Trudeau ya nemi Shugaba Buhari da ya tura ‘yan Najeriya “a karkashin wani shiri na musamman ga ‘yan ci-rani”.
An yada labarin kusan sau 2,500 a Facebook da kuma sauran shafuka daban-daban ciki har da zauren Yellow Vests Canada group, wanda ke da mabiya sama da 100,000 kamar yadda manhajar CrowdTangle mai kididdigar ayyuka a shafukan sada zumunta ta bayyana.
Shahararren dan jarida Dele Momodu da kuma tsohon dan takarar shugabancin kasa
sun yada adireshin labarin, wanda kuma aka sake yada shi sama da sau 500 a Twitter.
Ofishin jakadancin kasar ta Canda a Najeriya ya musanta labarin da cewa “wannan labari ba gaskiya ba ne” a shafinsa na Twitter, inda ya kara da cewa “‘yan Najeriya za su iya neman izinin shiga kasar ta hanyoyin da suka dace.”
Da alama yawan mutane miliyan daya da ake magana ya samo asali ne daga wata sanarwa da kasar ta fitar cewa tana so ta kara yawan wadanda take bai wa izinin zama a kasar zuwa miliyan daya cikin shekara uku masu zuwa.
Shirin kasar Canada na Canadian Federal Skilled Worker, wanda yake bai wa kwararru a fannoni da dama damar aiki a kasar yana da farin jinni sosai, kuma akwai ‘yan Najeriya da yawa da suka shiga kasar ta wannan hanya.
A shekarar 2016 mutum 42,430 ne suka bayyana kansu a matsayin ‘yan ci-rani daga Najeriya a kasar, wadanda sama da rabinsu ke zaune a babban birnin kasar Ontario.