Mun bi diddigin labaran da wasu mutane suka rinka yadawa kan lafiyar gwamnan da kuma inda ya shiga.
Mutane da dama sun yada hoton wani dattijo a kan gadon marasa lafiya a asibiti, wanda suka yi ikirarin cewa gwamnan jihar Kano ne Abdullahi Umar Ganduje.
Hoton, wanda ya karade shafukan sada zumunta, yana nuna mutumin da aka ce Ganduje ne kwance a asibiti, inda kuma mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna yake zaune a kan kujera lokacin da ya je dubiya.
An kuma yada hoton a zaurukan tattaunawa da dama a dandalin Whatsapp.
Sai dai a binciken da shafin Bindiddigi ya gudanar ya gano cewa maras lafiyar da ke kwance kan gado a cikin hoton ba gwamnan jihar Kano ba ne.
Hoton ya samo asali ne daga wani bidiyo da aka wallafa a shafin Youtube a ranar 21 ga watan Afrilu.
An yi wa bidiyon kanun; “Muna addu’ar Allah ya bai wa wannan bawan Allah lafiya bisa lalurar da take damunsa,” ba tare da bayyana sunan maras lafiyar ba.
Sai dai mun gano cewa Alhaji Yahaya Umar Bagobiri, wani jigo a jam’iyyar APC mai mulkin jihar, wanda ya sauya sheka kwanan nan daga PDP, shi ne mara lafiyar da Gawuna ya je dubawa ba Ganduje ba.
Ina Ganduje yake?
Binciken da Bindiddigi ya yi ya gano cewa Gwamna Ganduje lafiyarsa kalau, kuma a yanzu haka yana kasar Saudi Arabiya domin aikin Umarah.
Shi ma Kwamishinan yada labarai na jihar ta Kano Mohammed Garba ya tabbatar da cewa gwamnan yana kasa mai tsarki.
Ganduje ya bar Najeriya a ranar Asabar, 13 ga watan Afrilu, a karon farko tun bayan da aka sanar da nasarsa a zaben gwamnan jihar Kano, inda ya samu wa’adi na biyu.
A don haka wannan hoton da ake yadawa da cewar Ganduje ne ba gaskiya ba ne.