Shafin Zambian Observer ne ya fara wallafa labarin tare da nuna cewa “tsohon ministan tsaron Sudan”.
Shafukan Intanet da ma’abota shafukan sada zumunta da dama ne suka yi ta yada wani hoto da suka yi ikirarin cewa na Kanar Ibrahim Chamsadine ne tsohon ministan tsaro na kasar Sudan. Sai dai bincike ya nuna cewa batun ba gaskiya ba ne.
Hoton yana dauke ne da wani ramammen dattijo, wanda aka ce Kanar din ne aka gano a wani gidan yari da ke karkashin wani masallaci, inda aka ce tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir ne ke tsare da shi tun shekarar 2008 bayan da aka bayyana mutuwarsa a shekarar a wani hatsarin jirgin sama.
Shafin Zambian Observer ya wallafa labarin ranar 3 ga watan Mayu, suka yi masa take da cewa: “Wannan shi ne Kanar Ibrahim Chamsadine ministan tsaron Sudan”.
Shafin yana cewa ne shi ne ministan tsaro a Sudan amma Shugaba Omar al-Bashir ya garkame shi a gidan yari a shekarar 1995 saboda yana adawa da shi.
Shafin The People’s News Africa ma ya yada hoton a Facebook tare da wani mutum sanye da kakin sojoji, inda su kuma suka ce Kanar Awad Ibn Auf ne ministan tsaron Sudan wanda aka tsare a 1995.
Binciken da sashen bin diddigin labarai na kamfanin dillancin labarai na AFP ya gudanar, ya gano cewa, an yada hoton sama da sau 1000 an kuma yi sharhi a kansa sau 700.
Sai dai AFP ya gano Janar Awad Ibn Auf ba ya cikin wadanda aka ce sun mutu a shekarar 2008. Hasali ma shi ne wanda ya sanar da tumbuke Omar al-Bashir daga kan mulki a watan Afrilun 2019 bayan zanga-zangar da ‘yan kasar suka shafe makwanni suna yi.
Daga baya kuma ya zama shugaban majalisar sojojin da ke mulki, kafin daga bisani ya yi murabus.
Mutumin da yake jikin hoton shi ne Janar Omar Zain al-Abdin, wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin siyasa na gwamnatin sojan.
Shi kuma Kanar Ibrahim Shamseddine ya mutu tun a shekarar 2001 a wani hatsarin jirgi da ya rutsa da manyan sojojin kasar ta Sudan, kamar yadda jaridu da dama suka ruwaito a ranar 4 ga watan Afrilun 2001.
Shi dai hoton dattijon da ake yadawa bincike ya nuna cewa ba shi da alaka da kasar Sudan kuma yana dauke ne da wani mutum da bala’in fari ya galabaita shi a yankin Turkana na kasar Kenya.
Wani dan jarida a kasar Kenya ne Roncliffe Odit ya dauki hotunan kuma ya wallafa su a shafinsa na Twitter ranar 18 ga watan Maris, 2019. https://twitter.com/RoncliffeOdit/status/1107785821858484225
Odit dan jaridar BBC ne kuma ya yi martani ga daya daga cikin irin wadannan labaran da aka yada yana cewa “ni ne na dauki wadannan hotunan da hannuna a Turkana, Kenya”.