Mutumin da ya wallafa ya jawo hankalin Sanata Ben Murray-Bruce tsohon sanata daga jihar ta Bayelsa.
Wani hoto da ke dauke da wasu yara ‘yan makaranta zaune cikin ruwa a ajin karatu ya karade shafukan sada zumunta, inda aka yada shi sama da sau 3,000 a Facebook da Twitter.
Sai dai hoton wanda aka ce a jihar Bayelsa ce ta Najeriya, an dauke shi ne a garin Kilifi na kasar Kenya a wurin da aka yi ambaliya a farkon wannan watan.
An yada daya daga cikin hotunan da aka wallafa a Facebook, wanda ya ce a Najeriya ne abin ya faru sau 2,700.
Wanda ya wallafa ya jawo hankalin Sanata Ben Murray-Bruce tsohon sanata daga jihar ta Bayelsa.
Wannan hoto dai, an kuma wallafa shi a wurare da dama, ciki har da dandalin Intanet na Nairaland da Stella Dimoko Korkus da kuma Twitter, inda aka sake yada shi sama da sau 700.
Ambaliyar ruwa a Kenya
Duk da cewa wasu sun yi watsi da shi a matsayin labarin kanzon-kurege, wasu sun yi ta sukar Sanata Murray-Bruce game da yadda ya yi ta kamfe kan Najeriya ta koma amfani da motoci masu amfani da lantarki alhalin ga halin da daliban firamare suke ciki a jiharsa.
Sai dai binciken da aka yi a shafin bincika hotuna na Google reverse image search ya nuna cewa hoton ba a Najeriya aka dauke shi ba, an dauke shi ne a kasar Kenya.
Makaloli da dama ne suka fito a matsayin sakamakon binciken, wadanda suke bayyana yadda mutanen mazabar Ganze a yankin Kilifi na Kenya suka nuna bacin ransu game da abin da ya faru a makarantar firamare mai suna Mangororomu Primary School.
A farkon watan nan ne aka yi ambaliya a yankin na Kilifi, inda ta raba mutane da
dama da mahallansu.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ne ya fara wallafa wannan makala.