Hoton asali yana nuna Atiku ne zaune yana kallon wasan kwallo tsakanin Najeriya da kasar Morocco.
Dubban mutane ne suka yada wani hoto a Faebook da Twitter wanda yake nuna Alhaji Atiku Abubakar yana kallon bikin rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu ta kafar talabijin.
An gurbata hoton ne domin a nuna Atiku yana kallon bikin rantsuwar, amma hoton na ainahi yana nuna tsohon mataimakin shugaban kasar ne yana kallon wasan kwallon kafa.
A ranar Laraba 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa a karo na biyu, kuma abin da ya sa kenan aka gurbata hoton da nufin cewa a ranar abin ya faru.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce wani magoyin bayan Buhari ne mai suna Mustapha Maigonjo ya wallafa hoton a Facebook ranar Laraba, wanda aka yada shi sama da 4,500.
An sake yada shi sama da 2,300 bayan da wani daban ya sake wallafa shi, inda mutane da dama suka yi amannar hoton na gaske ne.
Kazalika, an kuma yada shi a Twitter cikin Turancin broka, inda wani ya yi wa Atiku da magoya bayansa ba’a.
Da aka yi bincike a shafin Google image search sai ga hoton Atiku ya bayyana, wanda aka wallafa shi a shafinsa na Twitter tun a Fabarairun 2018.
Hoton yana nuna Atiku ne zaune yana kallon wasan kwallo tsakanin Najeriya da kasar Morocco.
Morocco ce ta cinye Najeriya da ci 4-0 a wasan karshen da suka buga a birnin Casablanca, kamar yadda Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya ta bayyana.
Alhaji Atiku Abubakar dai ya yi watsi da sakamakon zaben da aka gudanar na Fabarairun 2019 kuma yanzu haka kotun sauraron korafe-korafen zabe tana sauraron karar da Atiku da jam’iyyarsa suka shigar.