Facebook bai bayyana yawan irin wadannan makaloli ba, ana iya cewa sun zama hantsi leka gidan kowa.
Facebook ya ce zai dauki matakin rage yawan tallace-tallace wadanda suka shafi magunguna da kuma cutuka a shafin, a wani yunkuri na dakile yaudarar da masu tallan ke yi domin jan hankalin masu amfani da shafin.
A wata sanarwa da shafin ya fitar ranar 2 ga watan Yuni, Fcaebook ya ce yana sane da cewa mutane ba sa son bayanai wadanda ake rubutawa domin zuzuta wani abu fiye da kima domin janyo hankalinsu.
Wadannan abubuwa sun hada da tallan magungunan wasu cutuka, inda wasu ke kambama girman cutar ko kuma maganinta, abin da Facebook din ya ce “yaudara ce kuma bai dace da dabi’ar al’ummar shafin ba”.
Matakan da za a dauka
A yunkurin kamfanin na kyautata kanun labarai da ke bayyana a harabar shafin masu amfani da shi wato News Feed, daga yanzu za a dakile makaloli wadanda aka kambama wata cuta fiye da kima a cikinsu da kuma wadanda ke kokarin sayar da wata hajarsu ta hanyar alakanta kansu da wata cuta.
Hanyoyi biyu ne dai za a bi wajen tantance irin wadannan abubuwa na yaudarar kamar haka:
- Idan makalar ta kambaba wata cuta ko maganinta. Misali: a ce akwai maganin komai-da-ruwanka
- Idan makalar ta yi tallan wata haja ta hanyar alakanta ta da wata cuta. Misali, maganin da ke rage kiba.
Abin da ake yadawar
Duk da cewa Facebook bai bayar da kididdigar yawan irin wadannan makaloli ba, ana iya cewa sun zama hantsi leka gidan kowa a dandalin.
Wani kwarya-kwaryar bincike da Bindiddigi ya gudanar ya gano cewa ana yada irin wadannan bayanai a-kai-a-kai musamman a shafukan kafafen yada labarai yayin da suka wallafa wani labari, inda ake saka su a matsayin martani domin mutanen da suke bin shafin su gani.
Wannan bayanin na kasa wani mai suna Oriajie Kate ne ya rubuta shi a karkashin wani hoto da shafin BBC Hausa ya wallafa a Facebook, inda yake zuzuta yadda ya samu sauki daga cutar kanjamau kuma yake so mutane su ziyarci daktan da ya ba shi maganin.
Wasu kuwa kan rubuta bayanai masu tsayi kan wasu cututtuka sai kuma su ce in kana son magani sai dai ka neme su a wata lamba daban, kamar wannan bayanin da Usman Abdullahi ya wallafa a shafin jami’ar Northwest University Kano Student Association.
Kazalika, wani mai suna GT Ramadan wallafa bayani ya yi a kan maganin karfin maza a zauren Asalin So Da Kauna ba tare da ya fadi suna ko inda za a samu maganin ba.
A madadin haka, ya bayar da lamba wadda za a tura masa katin waya kafin a samu karin bayani.
Shi ma Abba Maiyanmata bayanan ya wallafa, inda ya lissafo sunayen magani har 21 wadanda ya ce na mata ne da yake sayarwa kuma a karshe ya rattaba lambobin waya domin a tuntube shi.
Irin wadannan bayanai ana wallafa su ne a wuraren da aka san cewa dimbin mutane suna ziyarta, kamar zaurukan jami’o’i da shafukan kafafen yada labarai har ma da shafukan shahararrun daidaikun mutane.
A mafi yawan lokaci abin da suke yadawar ba shi da alaka da maudu’in da ake tattaunawa a wuraren da suke rubutawa, abin da Facebook ya ce zai dakile shi kamar yadda ya dakile bayanan yaudara da ake wallafawa, inda taken bayanin daban kuma abin da yake cikin adireshin daban.