Tuni dai kamfanin na NNPC ya rufe karbar takardun neman aikin, wanda aka fara a farkon shekaran nan.
A ‘yan kwanakin nan wasu mutane suka rinka yada wani sako ga jama’a musamman ‘yan arewacin Najeriya, inda ake kiran da su fito su nemi aiki a kamfanin mai na kasar, wato NNPC.
Sakon wanda aka rinka watsa wa ta manhajar WhatsApp, ya yi ikirarin cewa shirin daukar aikin na NNPC “ya bar ‘yan arewa a baya, a don haka ake kiran da su tashi su nema domin ka da a yi babu su”.
Sai dai binciken da muka yi ya nuna cewa tuni NNPC ya rufe karbar takardun neman aikin, wanda aka fara a farkon bana.
Bayanan da Bindiddigi ya tattara sun nuna cewa tuni aka rufe wannan shiri na daukar ma’aikata, kuma NNPC ya yi nisa wurin tantancewa da kuma ganawa da wadanda suka aika da takardunsu.
Abin da ya rage kusan za a iya cewa shi ne bayyana sunayen wadanda suka yi nasara.
“Wannan tsohon labari ne… a baya hakan ta faru [an samu karancin ‘yan arewa a jerin wadanda suka aika takardun neman aikin] amma yanzu an wuce wannan matakin;” a cewar wani babban ma’aikaci a NNPC.
- Amurka da Birtaniya ba su kauracewa rantsar da Buhari ba
- Buba Galadima bai fadi gaskiya ba kan ‘yarsa
- Kure-karya: WHO ba ta hana ‘yan kudu cin naman arerwa ba
Da muka ziyarci shafin na NNPC, mun fahimci cewa wadanda suka riga suka aika takardunsu tun asali ne kawai za su iya shiga domin duba matsayinsu, amma ba sababbin masu neman aiki ba.
A takaice, binciken da muka yi ya nuna cewa wannan sako da ake yadawa ba gaskiya ba ne, domin tuni NNPC ya rufe karbar takardun masu neman aikin.
Batun daukar aiki musamman na gwamnati a Najeriya, lamari ne da ke yawan haifar da ce-ce-ku-ce kan kabilanci da bangaranci, inda al’ummar kasar daban daban kan zargi juna da mamaye guraban ayyukan.
Hakan ne ya sa irin wadannan sakonni da ake aikawa kan yadu kamar wutar-daji, inda wasu masana ke ganin suna kara rura wutar kabilanci da kiyayya a kasar.