An kirkiri wadannan shafukan ne a kasashe kamar Daular Larabawa wato UAE da China da kuma Sifaniya.
Kamfanin sada zumunta na Twitter ya ce ya rufe shafukan masu amfani da dandalin har 4,000 bisa zarginsu da yunkurin cusa wa mutane wata manufa.
Kamfanin ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, inda ya ce shafukan na da alaka ne da gwamnatoci da ake amfani da su domin yada farfaganda.
An kirkiri shafukan ne a kasashe kamar Daular Larabawa wato UAE da China da kuma Sifaniya.
Shafukan China wadanda suka rika kokarin haddasa rigima tsakanin masu zanga-zanga a Hong Kong, da kuma na kasar Masar da Daular Larabawa masu magana kan Qatar da Yemen, su ne aka toshe, in ji Twitter.
- Ba a tallan cewa Buhari ya yi magudin zabe a Landan
- NNPC bai sake bude shafin daukar ma’aikata ba
- Buba Galadima bai fadi gaskiya ba kan ‘yarsa
An kuma rufe wasu shafukan daga kasashen Sifaniya da Ecuador, kuma kamfanin ya ce hakan yunkuri ne na kara fahimtar da mutane game da yadda wakilan gwamnatoci ke amfani da dandalin domin zambatar jama’a.
Twitter ya ce ya gano shafuka kusan 4,302 daga China da ke kokarin hada husuma tsakanin masu zanga-zanga a Hong Kong, abin da ya biyo gano karin wasu 200,00 a China din na ‘yan tada-zaune-tsaye.
A watan da ya gabata ma Facebook ya gano wasu shafuka a dandalin daga kasashen Masar da Saudiyya da Daular Larabawa, wadanda ke wallafa labaran karya kan wuraren da ake tashin hankali irinsu Libya da Sudan da Yemen.