Masu yada irin wadannan labarai sun fahimci cewa mutane sun fi yarda da su idan suka gurbata gaskiya.
Kwararru a fannin yaki da labaran boge na ci gaba dsa yin karin haske kan yadda masu wannan dabi’a ke kara bullo da sabbin dabaru, wanda suka hada da cakuda karya da gaskiya.
Labaran karya ba karya ba ce tsagawaro, a cewar Claire Wardle, daraktan cibiyar First Draft US, wacce ke yaki da irin wannan dabi’a.
“Muna shaida wa da idonmu yadda ake sauya wa ma’ana gurbi da kuma mayar da ita makami” kamar yadda ta ce a wata makala game da tsage gaskiya da kuma gina yarda a zamanin intanet.
Ita kanta kalmar ‘fake news’ ba ta kunshi dukkanin abin da ake nufi da labaran karya ba.
Da yawa daga cikin labaran da ake yadawa ba karya ba ce tsagwaro, labarai ne na gaskiya da ake gurbatawa tare da sauya masu fuska.
Masu aikata hakan sun fahimci cewa mutane sun fi yarda da su cikin sauki idan suka gurbata gaskiya sama da su kirkiri karya.

Claire Wardle ta cibiyar First Draft mai yaki da labaran karya
Kuma ba zai ma yiwu a kira su da labarai ba saboda mafi yawansu tsofaffin hotuna ne da bidiyo ake lalubowa a sauya masu fasali domin zambatar mutane.
Zumudin da muke da shi game da intanet ya sa muke tunanin cewa abubuwan alkairi ne kawai za su rika faruwa a intanet din musamman yadda muke samun bayanai cikin sauki da kuma saduwa da mutane cikin kankanin lokaci.
Sai dai wannan fahimtar an dade da gurbata ta sannan kuma yanzu ta fi raba mutane maimakon sadar da mu da junanmu.
Misinformation, disinformation, malinformation
Labaran karya suna da sunan yanka har guda uku: Misinformation, disinformation, malinformation, wadanda dukkaninsu suke alamta gurbata gaskiya zuwa wani abu daban.
‘Disinformation’ yana nufin wasu bayanai da aka yada na karya da gangan domin a yaudari jama’a.
Ana yada su saboda dalilai uku: domin a samu kudi ko tasirin siyasa na cikin gida ko na waje; ko kuma kawai domin haddasa fitina.
‘Misinformation’ ana yada shi ne kawai saboda dalilai na zamantakewa zalla. Kowanne mutum yana aikata al’adun kabilarsa ne a intanet.
Kowa yana so ya alakanta kansa da al’ada ko kabilarsa ko da hakan na nufin ‘yan jam’iyyarsu ta siyasa ko addini.
‘Malinformation’ wannan yana nufin bayanan da aka yada kawai domin a yi wa wani keta.
Misali shi ne, idan wani aboki ya yada wani gurbataccen bayani game da abokinsa domin bata masa suna. Wannan ya fi kamari tsakanin ‘yan siyasa da magoya bayansu.
Wajibi ne mu fahimci cewa yin amfani da abin da yake na gaskiya ne domin aika sakon rashin gaskikya ya fi sauki sama da a kirkiri sabo fil.
Wannan wani bangare ne na makalar da cibiyar First Draft US ta wallafa, wadda Claire Wardle ta rubuta.