An shafe bayanai miliyan 11 na lalata kananan yara a shafin Facebook da kuma 754,000 a Instagram.
Dandalin sada zumunta na Facebook ya share shafukan bogi biliyan 3.2 da aka kirkira a cikinsa a tsakanin watan Afrilu zuwa Satumbar wannan shekarar. Haka kuma Facebook ya goge miliyoyin bayanai da suke nuna cin-zarafin kananan yara da kuma kunan bakin-wake da aka wallafa a dandalin.
Wadannan bayanai suna kunshe ne cikin rahoton tantancewa na baya-bayan nan da kamfanin ya fitar.
Kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya hakaito, rahoton ya bayyana cewa an sami shafukan bogi fiye da rubi biyu na wadannan alkaluma wanda dandalin na Facebook ya shafe a shekarar da ta gabata.
A yayin da aka share shafuka biliyan 1.55 kamar yadda rahoton ya jaddada.
Dandalin na sada zumunta mafi girma a duniya ya sanar a karo na farko, adadin yawan bayanan bogi da aka wallafa kuma ya share a kafar yada hotuna ta Instagram wadda masu bincike akan yada labaran kanzon kurege ke nuna damuwarsu bisa la’akari da irin tasirin da take da shi na yayata irin wadannan bayanai.
Matakan kandagarki akan bayanan da suka karya ka’ida suna da karanci akan nau’ikan bayanan da ake wallafawa a dandalin Instagram fiye da na dandalin Facebook inda kamfanin ya dade da gabatar da irin wadannan matakai kamar yadda ya fada a kaso na hudu cikin rahotonsa na tantancewa.
Alal misali, Kamfanin ya sanar da cewa, ya gano wasu bayanai masu alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda har kaso 98.5 cikin dari na irin wadannan bayanai a dandalin facebook da kuma kaso 92.2 cikin dari a dandalin Instagram.
An shafe bayanai fiye da miliyan 11.1 da suke nuna tsiraici da lalata kananan yara a dandalin Facebook da kuma 754,000 a Instagram a zango na uku na shekara.
Matakan doka da dandalin na facebook ya ke son dauka na tabbatar da sirrin bayanai ga masu yadasu ta hanyar killace bayanan zai iya cutar da kokarin da ake na yakar cin-zarafin yara.
A watan da ya gabata, Daraktan Facebook, Christoper Wray ya sanar da cewa wadannan canje-canje za su canja dandalin zuwa abinda ya bayyana “gaskatar mafarkin mahara da masu yayata cin-zarafin kananan yara”.
Facebook ya kara sanya matakai akan hanyoyin sarrafa bayanai da ya hada da yadda mutum zai iya cutar da kansa a karon farko cikin rahoton nasa.
Ya kuma share bayanan da aka wallafa kimanin miliyan 2.5 wadanda suke nuna kunar bakin-wake da ji wa kai rauni a zango na uku na shekara.
Haka nan kamfanin ya goge bayanan da aka wallafa kimanin miliyan 4.4 wadanda suka kunshi hada- hadar miyagun kwayoyi a wannan gabar.