Muna fatan jama’a za su guji yada labarai marasa tushe. A tantance labarin da aka samu kafin a yada.
Shekarar 2019 da ta shude na sahun gaba a jerin shekarun da suka wahalar da masu fafutukar yaki da labaran karya musamman saboda wasu manya-manyan abubuwa da suka faru a cikinta a ciki da wajen Najeriya.
A Najeriya an gudanar da babban zaben kasar a farkon shekarar – wanda zabe na daga cikin abubuwan da suka fi haifar da labaran karya ko kuma ake amfani da su wurin yaudarar jama’a musamman masu zabe.
Baya ga Najeriya, a duniya baki daya ma an samu muhimman abubuwa kamar zaben Birtaniya, da batun tsige Shugaban Amurka Donald Trump da tashe-tashen hankula a yankin Kashmir na Indiya da kuma Sudan.
Duka wadannan abubuwa sun baiwa masu miyagun dabi’ar watsa labaran karya damar cin kasuwa, sai dai masu yunkurin tsaftace harkar yada labarai kamar Bindiddigi da sauransu basu yi kasa a gwiwa ba.
Mun yi waiwaye kan wasu muhimman batutuwa guda biyar na karya da aka bankado tare da fayyace gaskiyarsu a shekarar 2019 a Najeriya:
Kwankwaso bai ce zai rushe masallaci ba
Wani labari da ya rika yaduwa kamar wutar-daji a lokacin zabukan gwamnoni a Najeriya a watan Maris shi ne na cewa tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso ya sha alwashin rushe masallatai idan har jam’iyyarsa ta PDP ta lashe zaben jihar.
Sai dai binciken da muka yi ya gano cewa labari ne na karya, kuma bayanan da muka wallafa sun wayar wa da mutane da masu zabe kai matuka kan wannan karya da wasu suka yi amfani da shafukan sada zumunta na BBC na boge wurin wallafawa.
Da gaske ne Buhari ya yi yunkurin kara aure?
An shafe kwanaki ana takaddama yayin da shafukan intanet a Najeriya suka cika da bayanan boge na cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai auri Ministarsa ta Harkokin Jin kai da ‘Yan Gudun Hijira, Sadiya Umar.
Abokan aikinmu na sashin Hausa na BBC sun wallafa wani labari mai ban sha’awa inda suka bi diddigin lamarin tare da fayyace karyar da aka rinka yadawa game da shugaban da kuma ministar.
Ba a neman Atiku a Dubai kan rikicin Boko Haram
Jim kadan kafin a rantsar da Shugaba Buhari a karo na biyu a watan Mayu, sai labari ya watsu a kafafen sada zumunta cewa mahukunta a Hadaddiyar Daular Larabawa na neman abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP a zaben Alhaji Atiku Abubakar bisa zarginsa da hannu a rikicin Boko Haram.
An alakanta labarin ne da jaridar Gulf News wacce ake wallafawa a can, sai dai binciken da muka yi ya bankado karyar da ke kunshe a labarin, inda muka gano cewa an sauya fasalin shafin jaridar ne ta hanyar amfani da wasu manhajojin kwamfiyuta.
- Kure-karya: Da gaske an kafa ‘Ma’ikatar biyan albashi da wuri’ a Gombe?
- Ba a tallan cewa Buhari ya yi magudin zabe a Landan
- ‘Yan tayar da zaune-tsaye sun yi min kage – Atiku
Atiku ko Buhari: Wa kasar Jamus ta goyi baya?
A lokacin da ake tsakiyar yakin neman zabe, sai labari ya barke a Najeriya na cewa Shugabar Jamus Angela Merkel ta ce “demokuradiyya karkashin gwamnatin Shugaba Buhari ita ce mafi kyau a duniya”.
Binciken da gamayyar ‘yan jaridu masu bin kwa-kwaf kan zaben Najeriya ta CrossCheck ta yi, ya gano cewa labarin na boge ne domin bashi da tushe ballantana makama.
Jaridar Vanguard ta yi amai ta lashe
A watan Satumba ne jaridar Vanguard ta Najeriya ta amince cewa ta wallafa labaran karya da suka jawo ce-ce-ku-ce a kasar kan mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo.
Jaridar ta zargi Osinbajo da laifin aikata ba daidai ba a wata badakala ta mukudan kudade a Hukumar Tattara Haraji ta kasa wato FIRS.
Sai dai daga bisani ta janye labarin tana mai cewa ta gano babu gaskiya a ikirarin nata. Tun da farko Mista Osinbajo ya yi barazanar daukar matakin shari’a kan wadanda suka watsa labarin.