Wasu ma’abota shafukan sada zumunta sun yi ta yada wasu hotuna da bidiyo da ke nuna shugaban kasar Sin wato China Xi Jinpin na ziyara a wani masallaci, inda suke danganta ziyarar da barkewar annobar cutar Coronavirus a kasar ta Sin.
Sakwannin da ake yadawa tare da hotunan a shafukan Facebook, twitter da Whatsapp na nuna cewa shugaban na kasar Sin ya ziyarci masallacin ne domin bukatar adduo’in al’ummar Musulmi don kawo karshen yaduwar cutar Coronavirus a kasar.
Sai dai binciken da Bindiddigi ya gudanar ta hanyar tantance hotunan da ake yadawa bisa amfani da fasahohin tantance hotuna a shafukan intanet, ya gano cewa hotunan da ake yadawa basu da alaka kwata-kwata da cutar Coronavirus, domin shugaban na Sin ya kai ziyara masallacin ne tun a shekarar 2016, a don haka tsofaffin hotuna ne ake yadawa yanzu ake kuma danganta su da cutar Corona Virus.
Wasu shafukan da ke ikirarin yada labaran gaskiya suma sun tsinci kansu a wannan dambarwa ta yada labaran na karya game da batun, ciki har da shafin Facebook na jaridar Rariya da ke da mabiya fiye da miliyan daya, da kuma shafin Dokin Karfe da ke da mabiya fiye da dubu dari biyar.
Shafin Rariya na Facebook ya yi wa nasa labarin ne taken” Yadda Bulluwar Cutar ‘Corona Virus’ Ta Dawo Da Martabar Musulman Kasar Chana”, kuma ma’abota shafin sun yada shi fiye da sau dubu daya da dari biyar kuma suka yi sharhi fiye da dari shida.
Shi ma shafin Dokin Karfeya yi wa nasa labarin take iri daya da na Rariya “Yadda Bulluwar Cutar ‘Corona Virus’ Ta Dawo Da Martabar Musulman Kasar Chana”, kuma ma’abota shafin sun yada shi fiye da sau dari da sittin, yayinda suka yi sharhi fiye da sittin, kuma mafi yawan sharhin na nuna cewa wadanda suka karanta labarin sun yarda da sahihincinsa, ba tare da sanin cewa labarin na karya ne ba.
Wannan na nuna cewa shafukan da ke yada labaran karya a wasu lokutan basu ma daddale wa jama’a ainihin majiyar su ta labarai, yayinda suke kwaikwayon junansu wajen yada labaran karya, kamar yadda muka gani a wannan misalin da ke sama tsakanin shafin na Rariya da na Dokin Karfe.
Banda hotunan shugaban na China da aka nuno shi a cikin masallaci, shafin Dokin Karfe ya kuma wallafa karin wasu hotunan na maza da mata suna sallah, sai dai binciken Bindiddigi ya gano cewa, Karin hotunan biyu ma ba su da alaka kwata-kwata da ziyarar shugaban. Hasali ma an fara wallafa hoton mazan da ke sallah ne a watan Yuli na shekarar 2015, yayinda aka fara wallafa hoton matan da ke sallah a watan Yuni na shekarar 2016.
Tuni dai shafin sada zumunta na Facebook ya bayyana cewa ya fara daukar matakai na dakile yada labaran karya game da cutar ta Coronavirus da ma sauran batutuwa, ta hanyar aiki tare da shafukan da ke bin diddigin labarai, domin rabe aya da tsakuwa don kare lafiyar al’umma a lokacin da ake kokarin shawo kan annobar cutar Coronavirus a kasashe daban-daban na duniya.