Shafin sada zumunta na Facebook ya sanar da cewa zai fara hana wallafa labaran karya game da allurar rigakafin cutar COVID-19, sai dai shafin ya kara da cewa ba zai iya aiwatar da wannan kudiri cikin kankanin lokaci ba.
Shafin ya fitar da wannan sanarwar ne bayan kasar Burtaniya ta zamanto kasa ta farko a duniya da ta amince da inganci da kuma fara amfani da allurar rigakafin cutar ta COVID-19 da kamfanin Amurka Pfizer da BioNTech na kasar Jamus suka samar domin amfanin gama-garin al’umma. A makwanni masu zuwa, shafin zai fara goge duk wani bayani da aka wallafa a Facebook ko Instagram da ya kunshi bayanan karya (da kwararrun lafiya suka karyata) game da allurar rigakafin COVID-19 don kaucewa cutar da al’umma.
Kamfanin na Facebook ya yi Karin bayani kan irin sakwannin da zai fara gogewa a wata sanarwa da ya wallafa: “Ga misali, za mu cire duk wani ikirari na bogi da ya kunshi cewa allurar rigakafin COVID-19 na kunshe da wasu naurori masu kwakwalwa mafi kankanta da ake kira “microchips”, ko kuma duk wani abu da ba ya cikin kayan hadin allurar rigakafin.”
An dai shafe watanni da dama ana sukar shafin na Facebook da sauran shafukan sada zumunta, saboda wasu na ganin sun gaza wajen daukar matakan dakile bayanan karya da aka yi ta yadawa game da cutar coronavirus.

COVID-19: Facebook zai fara goge labaran karya game da allurar rigakafi
Shafin sada zumunta na Facebook ya sanar da cewa zai fara hana wallafa labaran karya game da allura
Manyan LabaraiPrimary category in which blog post is published