cropped-820x461-22.jpg

Wannan shi ne Shafin Farko da ke bin Diddigin labaran da ake tababa kan sahihancinsu, don tantance gaskiya da karya da harshen Hausa. Bindiddigi shafi ne da kwararrun ‘yan jarida suka samar domin habaka aikin tantance gaskiya da karya a labaran da ake yadawa a shafukan intanet, musamman shafukan sada zumunta wato soshiyal midiya.

 

Ma’aikatanmu sun kware matuka kasancewar sun yi aiki a manyan kafafen yada labarai a ciki da wajen Najeriya a fannoni daban-daban na aikin jarida.

 

A baya-bayan nan mutane kan shiga rudani game da gaskiya ko karyar wasu bayanan da ake yadawa a shafukan sada zumunta, saboda yawaitar labaran karya da mutane ke kirkira su kuma yada su. Samuwar shafukan sada zumunta sun saukaka wa wasu mutane da suke kirkirar irin wadannan labaran su kuma yada su kamar wutar daji.

 

A don haka, shafin Bindiddigi ya fito domin ya bada tasa gudummawar wajen tantance gaskiya ko karyar irin wadannan bayanai da ke yaduwa a shafukan sada zumunta na soshiyal midiya.

 

Yadda muke tantance labari

 

A aikin tantance gaskiyar labarai, shafin Bindiddigi na yin amfani da kwarewa da ka’idojin aikin jarida, na ba sani ba sabo, da rashin nuna bangaranci.Mukan bibiyi bayanan da aka yada a shafukan intanet ko shafukan sada zumunta (da ake tababa kan sahihancinsu) domin tantance hakikanin ikirarin da aka yi a cikinsu.

 

Mukan duba hujjojin da aka gabatar, sannan mu tuntubi wadanda suka yi ikirarin domin su gabatar da hujjojinsu, idan da bukata, mukan bincika ingantattun kundayen adana bayanai don tabbatar da ingancin ikirarin.

 

Wasu lokutan muna tuntubar kwararru domin su bayar da nasu bahasin game da batun, sannan mu rubuta sakamakon bincikenmu, mu kuma wallafa shi a shafin Bindiddigi.

 

Za mu kuma rinka kawo muku bayanai na ilimantarwa kan hanyoyin da za ku rika bi wurin tantance labaran karya ko masu rikitarwa wadanda a kan watsa a sassan duniya daban-daban.

 

Za ku iya turo mana labaran da suka shige muku duhu ko kuke tababa a kan inganci ko sahihancinsu domin mu bi muku diddiginsu.Za ku iya tuntubar mu ta adireshinmu na Email bindiddigi@gmail.com

 

Ko kuma ta WhatsApp a lamba: +234 902 745 0542

 

Twitter: @bindiddigi

 

Facebook: Bindiddigi Sai mun ji daga gareku.